✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kame ‘yan kungiyar asiri 100 da makamai a Legas

Hukumar ‘yan sandan Jihar Legas, ta kame wasu mutum 100 tare da kwace makamai a hannun su wadanda a ke zargin ‘yan kungiyar asiri ne,…

Hukumar ‘yan sandan Jihar Legas, ta kame wasu mutum 100 tare da kwace makamai a hannun su wadanda a ke zargin ‘yan kungiyar asiri ne, a tsakanin ranakun Lahadi da kuma Litinin na makon nan a jihar Legas.

Kamar dai yadda Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Zubairu Mu’azu ya bayyana a jiya Talata.

Kwamishinan, wanda ya gabatar da mutanen gaban manema labarai, a birnin Legas din, ya ce an yi kamen ne bayan bayanan sirri da Hukumar ta samu, kan shirinsu na gudanar da bikin ranar yaki da ‘yan kungiyar asiri a jihar.

Ya ce, an kame ‘yan asirin su 100, a ciki da kewayen birnin Legas, yayin da aka gurfanar da 70 cikin su gaban shari’ah, ana ci gaba wasu 30 din kuma ana bincikensu.

“Mun gano kungiyoyin asiri da wasu gungun masu aikata miyagun laifuka a sassa daban-daban na jihar, kuma muna tunkarar su har zuwa maboyarsu”. In ji Kwamishina Mu’azu.