✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kammala bikin karrama mawakan zamani na duniya

A Lahadin da ta gabata ce aka kammala bikin karrama mawakan zamani na duniya, inda fitattun mawaka suka samu kyaututtukan karramawa daban-daban.Bikin karramawar, mai taken…

Mawaqi Justin Timberlake, rungume da tarin kyaututtukan da ya ci a bikin MTV na banaA Lahadin da ta gabata ce aka kammala bikin karrama mawakan zamani na duniya, inda fitattun mawaka suka samu kyaututtukan karramawa daban-daban.
Bikin karramawar, mai taken ‘MTb bideo Music Awards, an gudanar da shi ne a Barclays Center a Brooklyn da ke New York na Amurka.
Kamar yadda sakamakon ya nuna, mawaki Justin Timberlake ne ya samu kyautar ‘Faifai Mafi Fice a 2013.’ Ya samu wannan kambi ne da faifan wakokinsa mai taken ‘Mirrors.’
Ita kuwa zabiya Taylor Swift, ta samu kyautar ‘Faifai Mafi Fice Na Mata.’ Faifan wakokinta mai taken ‘I Knew You Were Trouble’ ne ya samar mata wannan kyauta.
Sauran wadanda da suka samu karramawa sun hada da Bruno Mars, saboda faifansa mai taken ‘Locked Out of Heaben.’ Akwai Selena Gomez, wacce ta samu karramawa da faifanta mai taken ‘Come & Get It.’ Ita ma kungiyar mawaka ta ‘Macklemore & Ryan Lewis’ mai dauke da faifan Ray Dalton mai taken  ‘Can’t Hold Us’ ta samu tata kyautar karramawar.
Haka kuma ‘Thirty Seconds to Mars’ sun samu kyauta da faifansu na ‘Up In the Air.’