Notice: Undefined index: show_thumbnails in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 199

Notice: Undefined index: show_headline in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 200
An kammala Gasar cin Kofin Super ta Kasa - Aminiya
Aminiya

An kammala Gasar cin Kofin Super ta Kasa

A farkon makon nan ne aka kammala gasar gwarzayen kungiyoyin kwallon kafa hudu na kasa da aka fi sani da Super 4. Gasar ta cin Kofin Super ta Kasa a bana an gudanar da ita ce a garin Enugu fadar Jihar Enugu. Kungiyar kwallon kafa ta Akwa Starlets ce ta dauki kofin bayan ta lallasa Kungiyar Adamawa United da ci biyu da nema. Yayin da Kungiyar Kwallon Kafa ta Jigawa Golden Stars ta zo ta uku bayan da ta samu nasara a kan abokiyar karawarta ta Warri Wolbes da ci 2-1.

Da yake bayani matashin dan wasan gaba na Kungiyar Jigawa Golden Stars Mujahid Ibrahim ya bayyana cewa gasar ta ba shi karin gogewa da kuma kwarin gwiwa, “A gaskiya duk da yake mu muka zo na uku a wannan gasa ta Super 4 ta Kasa a bana, ina cike da farin cikin samun damar buga wannan gasa domin kuwa ta kara mini gogewa tare da ba ni kwarin gwiwar taka leda domin in gwada basirar da nake da ita,” inji shi.