✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kammala jigilar mahajjatan Yobe

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Yobe, Alhaji Bukar Kime ya ce dukkan mahajjatansu sun isa Kasa Mai tsarki. Alhaji Bukar Kime ya ce…

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Yobe, Alhaji Bukar Kime ya ce dukkan mahajjatansu sun isa Kasa Mai tsarki.

Alhaji Bukar Kime ya ce kuma dukkan mahajjatan  sun isa Saudiyya ba tare da wata matsala ba, baya ga wadda suka samu a wajen tantance su a sansanin alhazai na garin Maiduguri  da yake a Jihar Borno suka tashi.

Ya ce suna da mahajjata 1,253 wadanda su ka biya wa kansu da jami’an hukumar da tawagar jami’an lafiya.

Ya jinjina wa gwamnatin Jihar Yobe kan yadda ta ba su katifu dubu daya da matasan kai da suka kwanta a sansanin alhazan da ke Maiduguri, inda ya ce a baya a kasa maniyyata suke kwanciya.

Sai ya yi kira ga maniyyatan su zamo jakadu nagari a lokacin da suke Kasa Mai tsarki su kuma guji zubar wa kasarsu kima a idon duniya.