Da Dumi Dumi

An kammala Musabakar Alkur’ani a yankin Jama’a

An kammala gasar Musabakar Alkur’ani Mai girma a garin Kafanchan inda dalibai 97 da suka hada maza da mata daga garuruwan da ke karkashin karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna suka fafata a matakai daban-daban.

Shugaban Majalisar Malamai Ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta gundumar Kafanchan, Malam Hamza Ibrahim Na-Kawu, wanda ya gabatar da mukala mai taken ‘Muhimmanci Karatun Alkur’ani da Falalarsa’, ya bayyana falalar da Alkur’ani ke dauke da shi da suka hada da kasancewarsa haske da alheri da natsuwa da shiriya kuma ceto ga masu karantawa da kuma aiki da shi.

Malamin ya yi kira ga dalibai su guji shagaltuwa da na’urorin zamani maimakon haka, su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace kuma su yi kokari alakarsu da Alkur’ani ta zamo tamkar alakarsu da wayar salula.

A karshe ya yi kira ga matasa su guji tu’ammuli da miyagun kwayoyi da sauran kayan maye sannan ya roki Gwamnatin Jihar Kaduna da ta karamar Hukumar Jama’a su rika bayar da gudunmawarsu ga makarantu da malamai da kuma daliban da ke karatun Alkur’ani.

A jawabin Mataimakin Shugaban Kwamitin Musabaka na Jihar Kaduna, Sheikh Tasi’u Ismail Sulaiman, Talban Kachiya, wanda ya isar da sakon Shugaban Kwamitin Musabaka na Jihar Kaduna Dokta Bello Abdukadir Salanken Zazzau, ya karfafi mutanen karamar hukumar ne kan su tashi tsaye su farfado da martabar da aka san su da ita a shekarun baya ta zama zakarun musabaka a jihar.

ADVERTISEMENT

Ko’odinetan Kwamitin Musabaka, Alhaji Bashir Idris da Shugaban Kwamitin na karamar Hukumar, Imam Mustafa Tahir, wanda Mataimakinsa Malam Aminu Nababa Tahir ya wakilta sun mika godiyarsu ga malamai da makarantun da suka shiga musabakar ta bana, wadanda adadinsu ya karu fiye da na bara da su kara zage damtse domin shirin fafatawa da takwarorinsu a matakin jiha da za a gudanar nan gaba.

Shugaban Alkalan Musabakar, Malam Abdullahi Musa Badembo ne ya jagoranci bayar da kyaututtuka a dukan matakan da aka fafata da suka hada da izifi goma da ashirin da arba’in da tanghimi da kuma izifi sittin ba tafsiri ga daliban da suka zo na daya zuwa na uku.

A karshe Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II wanda Sarkin Gandun Jama’a, Alhaji Sulaiman Isa ya wakilta ya bayyana farin cikinsa kan gudanar da wannan aikin alheri na hidima ga Alkur’ani a masarautarsa inda ya yi fatan alheri ga masu shirya gasar da daliban da suka fafata a musabakar.

Hauwa’u Muhammad da Abubakar Muhammad ne suka zamo gwarazan musabakar a matakin izifi sittin ba tafsiri inda aka nada su a matsayin Zakarun Musabakar 2018 na karamar hukumar.

Share