Gwamnatin Tarayya ta sanar da kara farashin man fetur zuwa N143.80 a kan kowacce lita.
Hukumar Kayyade Farashin Mai ta Kasa (PPPRA) ta bayyana haka a wata sanarwa a ranar Laraba.
Sanarwar da aka raba wa dillalan mai dauke da kwanan watan daya ga watan Yuli ta ce, “Bayan la’akari da yanayin kasuwar mai a watan da ya gabata da kuma nazarin halin da dillalai suke ciki, muna bayar da shawarar a kara farashin mai zuwa tsakanin N140.80 da N143.80 daga farkon watan Yulin 2020.
“Mun umarci dukkan dillalai da su sayar da man a tsakanin wadannan farashin kamar yadda PPPRA ta ba da shawara.
Kusan sau uku hukumar tana rage farashin man a bana sakamakon faduwarsa a kasuwar duniya, ko da yake wannan ne karon farko da aka kara kudinsa a shekarar da muke ciki.