✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kara wa ‘yan sandan da aka kashe a zanga-zangar #EndSARS matsayi

Ya ce karin girman wata hanya ce ta yabawa irin sadaukarwar su wajen hidimtawa kasa lokacin da suke raye.

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da karin matsayi ga jami’an ’yan sanda 16 da aka hallaka yayin zanga-zangar #EndSARS.

Ya ce karin girman wata hanya ce ta yabawa irin jajircewa da kuma sadaukarwar su wajen hidimtawa kasa lokacin da suke raye.

Mohammed ya kuma amince da yin karin matsayi ga wasu kananan jami’an rundunar guda 82,779 zuwa matsayin matakansu na gaba.

Kakakin rundunar, Frank Mba a cikin wata sanarwa  a ranar Litinin ya ce karin girman ya hada da jami’ai 56,779 da aka daga likkafar su daga mukamin Sajan zuwa na Insfekta; 17,569 daga Kofur zuwa Sajan; da kuma 8,431 daga Konstabul zuwa Kofur.

A cewarsa, karin girman na daya daga cikin irin kokarin rundunar ke yi na kara wa jami’anta kwarin gwiwar yin aiki yadda ya kamata.

“Wadanda aka kara wa girman sun hada da kananan jami’ai 86 wadanda rikicin masu zanga-zanga ya shafa, 16 daga cikin wadanda aka kashe sun sami karin girma yayin da wasu 70 kuma da suka sami munanan raunuka saboda zanga-zangar #EndSARS suma sun sami karin girman.