✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karbo daga Abu Ma’amar ya ce:

341. An karbo daga Abu Ma’amar ya ce: “Abdul Waris ya ba mu labari, daga Abu Tayyah daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa:…

341. An karbo daga Abu Ma’amar ya ce: “Abdul Waris ya ba mu labari, daga Abu Tayyah daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Annabi (SAW) ya iso Madina ya yi umarni da ginin masallaci sai ya ce: “Ya kabilar Bani Najjar ku sanya mini kudin filayenku.” Sai suka ce, “Ba mu neman kudinsu face a wurin Allah (mun bayar domin Allah).” Sai (Annabi) ya yi umarni aka baje kaburburan mushirikai. Sa’an nan aka daidaita tsofaffin kangaye, dabinai aka sare su aka yi sahu da dabinai ta wajen alkiblar masallaci.”
342. An karbo daga Isma’ilu dan Abdullahi ya ce: “dan uwana ya ba ni labari daga Sulaiman daga Ubaidullahi daga Sa’idul Makburi daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “An haramta abin da ke tsakanin laba biyu (tsaunukan nan biyu) a bisa harshena.” (Abu Huraira) ya ce, “Annabi (SAW) ya tafi ga Bani Harisa sai ya ce, “Lallai ni, ina ganinku ya kabilar Bani Haris kun fita daga hurumin Madina, sa’an nan sai ya sake waiwaye ya ce, “A’a, kuna cikinsa.”
343. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “Abdurrahman ya ba mu labari ya ce, Sufiyan ya ba mu labari daga A’amashi daga Ibrahim Tamimi daga Babansa daga Aliyu (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Babu komai gare mu face Littafin Allah da wannan takarda daga Annabi (SAW) cewa: “Madina haramun ce daga A’iru zuwa kaza, wanda ya kirkiri wata bidi’a cikinta ko ya taimaki (saukar da) dan bidi’a to la’anar Allah tana kansa da mala’iku da mutane gaba daya. Ba a karbar masa wani aikin farilla ko adalci (nafila). Kuma (Annabi) ya ce, “Mutuncin Musulmi duka daya ne, wanda ya wulakanta (yaudari) wani Musulmi, to, la’anar Allah tana kansa da mala’iku da mutane gaba daya. Ba a karbar masa wani aikin farilla ko adalci. Wanda ya shugabanci (mulki) wasu mutane (bayin Allah) ba tare da izinin shugabansu ba la’anar Allah tana kansa da mala’iku da mutane gaba daya. Ba a karbar masa wani aikin farilla ko na nafila (adalci).” Abu Abdullahi ya ce, “Ma’anar adalci wani fansa.”

Babi Na Biyu: Fifikon Madina kuma lallai ita, tana korar miyagun mutane:
344. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Yahya dan Sa’id ya ce, “Na ji Abu Hubab Sa’id dan Yassar yana cewa: “Na ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce an umarce ni da tafiya zuwa wata alkarya wadda take cikin sauran alkaryu, suna ce mata Yasriba ita ce Madina, tana korar miyagun mutane kamar yadda wutar makera ke fitar da daudar bakin karfe.”

 Babi Na Uku: Madina Dabat ce, (abar faranta rai):
345. An karbo daga Khalid dan Makhlad ya ce: “Sulaiman ya ba mu labari ya ce, Amru danYahya ya ba ni labari daga Abbas dan Sahlu dan Sa’ad daga Abu Humaid (Allah Ya yarda da shi) ya ce; “Mun fito daga Tabuka tare da Annabi (SAW) zuwa Madina. Har sai da muka fara hangen Madina sai (Annabi) ya ce: “Wancan itace, Dabat (abar farin ciki).”

Babi Na Hudu: Abin da ke tsakanin tsaunuka biyu na Madina:
346. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Sa’id dan Musayyab daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai shi ya kasance yana cewa: “Ko da zan ga barewa a Madina tana kiwata abin farautarta. Saboda Manzon Allah (SAW) ya ce: “Abin da ke tsakanin tsaunukan nan biyu na Madina haramun ne.”