Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An karbo daga Ahmad danYunus ya ce:

317. An karbo daga Ahmad danYunus ya ce: “Ibrahim dan Sa’ad ya ce, dan Shihab ya ba mu labari daga Salim daga babansa Abdullahi (Allah Ya yarda da shi) cewa; “An tambayi Manzon Allah (SAW) cewa: Me mai harami zai sanya daga tufafi? Ya ce, “Kada ya sanya riguna ko rawunna ko wanduna ko alkyabbu. Kuma kada ya sanya tufafin da turaren Zafaran ko Warasu ya shafe su. Idan mai harami bai samu takalma marasa rufi ba, to yana iya sanya Khuffi amma sai ya yanke karkashinsu kasa da idon sawu (kafa).”
 
Babi na Goma Sha Shida:
Wanda bai samu gyauto ba, sai ya sanya wando
318. An karbo daga Adamu ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari ya ce, Amru dan Dinar ya ba mu labari daga Jabir dan Zaid daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya yi mana huduba a Arfa sai ya ce: “Wanda bai samu gyauto ba, to yana iya sanya wanduna. Wanda bai samu dangarafai (takalma mara rufi) ba, sai ya sanya Khuffi (takalmin fata masu rufe kafa har zuwa kwauri).”

ADVERTISEMENT

Babi na Goma Sha Bakwai:
Rataya makami (takobi) ga mai harami. Ikramata ya ce, “Idan mutum ya ji tsoron abokin gaba sai ya dauki makamai, amma zai biya fansa. Amma babu malaman da suka yarda da hukuncinsa (Adda’u).

319. An karbo daga Ubaidullahi daga Isra’ilu ya ce: “Daga Abu Is’hak daga Barra’u (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya yi Umara a watan Zul kida sai mutanen Makka suka ki barinsa ya shiga Makka face bisa yarjejeniyarsu. Bai shigo Makka da makami (takobi) ba, face a cikin kubensa.”

ADVERTISEMENT

Babi na Goma Sha Takwas:
Shiga yanki na Harami da Makka ba tare da Ihrami ba. dan Umar ya shiga ba tare da Ihrami ba, saboda Annabi (SAW) ya yi umarni da Ihrami ne ga wanda yake son Ihramin Hajji da Umara. Amma bai ambaci hana shigar masu sana’ar sarar itace ba da makamantansu (masu aikin harami).”
 
320. An karbo daga Muslim ya ce: “Wuhaib ya ba mu labari ya ce, dan dawus ya ba mu labari daga Babansa daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya sanya wuri (mikati) ga mutanen Madina daga Zul Hulaifa. Ga mutanen Najad kuma daga karnul Manazil. Ga mutanen Yaman kuma daga Yalamlam, ya sanya su gare su, tare da dukkan wanda ya zo ta kansu daga waninsu ga wanda ya yi nufin Hajji ko Umara. Wanda ya kasance koma bayan haka to shi daga duk inda ya faro har mutanen Makka su faro daga Makka.

321. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya shiga Makka a shekarar cin Makka da yaki. A bisa kansa da Migfar (malfar kwano) lokacin da ya cire ta, sai wani mutum ya zo ya ce: “Lallai ga dan Khadal can na rataye da rufin (labulen bango) Ka’aba. Sai (Annabi) ya ce: “Ku kashe shi.”

Babi na Goma Sha Tara:
Idan jahili ya yi Ihrami da aikin Hajji ko Umara alhali na sanye da taguwa (sai ya tube, ko akwai fansa a kansa)? Adda’u ya ce, “Idan mutum ya sanya turare ko taguwa da jahilci, ko da mantuwa babu kaffara (fidiya) a kansa.”
322. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Hammam ya ba mu labari ya ce, Adda’u ya ba mu labari ya ce, Safwan dan Ya’alah ya ba mu labari daga Babansa ya ce: “Na kasance tare da Manzon Allah (SAW) sai wani mutum ya zo masa yana sanye da wata kubta (alkyabba) kuma a cikinta da launin turare Sufr ko ya ce, kamar haka. Umar ya kasance yana fada mini cewa: Shin kana son ka ga lokacin da wahayi ke sauka gare shi (Annabi)? Ana nan haka sai wahayi ya sauka masa, sai aka yaye (kuranye) masa sai ya ce: “Ka aikata cikin Umararka kamar yadda kake aikata wa a Hajjinka.” Ana nan haka kuma sai ga wani ya caki yatsun dan uwansa har ya cire masa hakorin gaba. Sai Annabi (SAW) ya bata hukuncinsa (diyyarsa).”