Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An karbo daga Sa’id dan Rabi’u ya ce:

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus
 Almashgool, Bauchi

ADVERTISEMENT

297. An karbo daga Sa’id dan Rabi’u ya ce: “Aliyu dan Mubarak ya ba mu labari daga Yahya daga Abdullahi dan Abu kattada cewa: Lallai Babansa ya ba shi labari ya ce: “Mun fita tare da Annabi (SAW) a shekarar Hudaibiyya, sai abokaina suka yi Ihrami, amma ni ban yi Ihrami ba. Sai aka ba mu labari da abokan gaba a Ghaikat saboda haka sai muka fuskanci ta wurinsu. Sai abokaina suka hangi jakin dawa, sai sashinsu suka rika dariya ga sashi, sai na waiwaya na gan shi, na kai masa hari bisa godiya na soke shi na kama shi. Sai na nemi taimakonsu suka ki taimakona. Sai muka ci daga gare shi, sa’an nan na yi kokarin haduwa da Manzon Allah (SAW) saboda mun ji tsoron kada a katse tsakaninmu da shi. Sai na rika zabura da gudu da abin hawata, sa’an nan na tafi kadan, sai na hadu da wani mutum daga kabilar Ghifar a cikin duhun dare, na ce: “Ina Manzon Allah (SAW)?” Ya ce, “Na bar shi a Ta’ahun yana nufin isa Sukya don ya huta.” Na iske Manzon Allah (SAW) har na isa gare shi, sai na ce, “Ya Manzon Allah! Lallai sahabbanka sun aiko da sallama a gare ka da rahamar Allah da albarkarSa. Kuma lallai su, sun ji tsoron kada abokan gaba su tsare tsakaninsu da kai, ko za ka saurara musu, sai (Annabi) ya aikata haka. Na ce, “Ya Manzon Allah! Lallai mu, mun yi farautar jakin dawa, kuma akwai saura a tare da mu.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce da Sahabbansa: “Ku ci”, alhali suna a cikin Ihrami.”

  Babi na Hudu: Mai Harami da aikin Hajji ko Umara ba shi taimakon mara Ihrami kashe abin farauta

ADVERTISEMENT

298. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari, ya ce, Salih dan kaisan ya ba mu labari daga Abu Muhammad ya ce: Ya ji Abu kattada, (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Mun kasance tare da Annabi (SAW) a wani wuri da ake kira ka’hah tafiyar zango uku daga Madina – Hawwala Sanad. Ya ce, “Aliyu dan Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Salih dan kaisan ya ba mu labari daga Abu Muhammad daga Abu kattada, (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mun kasance tare da Annabi (SAW) a ka’hah daga cikinmu akwai masu Ihrami da wadanda ba su da Ihrami, sai na ga abokaina kamar na kallon wani abu, sai na waiwaiya na ga jakin dawa. Sai na ruga da gudu makamina (mashi) ya fadi. Na roki su taimaka su miko mini suka ce, “Ba za mu taimake ka da komai ba, saboda muna da Harami, sai na yi kokarin daukarsa kuma daga karshe na dauke shi. Sa’an nan na bi shi (jakin) daga bayan Akama (karamin tudu, ko tsauni) na soke shi, na zo da shi ga abokaina. Wasu suka ce, “Ku ci”, wasu suka ce, “A’a, kada ku ci.” Sai na tafi da shi zuwa ga Annabi (SAW) yana gaba gare mu, na tambaye shi, sai ya ce: “Ku ci, shi halal ne.” Amru ya ce, “Ku tafi zuwa ga Salih ku tambaye shi game da wannan da waninsa, suka iso gare mu a nan.”