✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karbo daga Yahya dan Sulaiman ya ce:

304. An karbo daga Yahya dan Sulaiman ya ce: “dan Wahab ya ba ni labari ya ce, Yunus ya ba ni labari daga dan Shihab…

304. An karbo daga Yahya dan Sulaiman ya ce: “dan Wahab ya ba ni labari ya ce, Yunus ya ba ni labari daga dan Shihab daga Urwata daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Dabbobi biyar dukkansu fasikai ne ana ka she su a cikin harami. Hankaka da shirwa da kunama da bera da mahaukacin kare.”

305. An karbo daga Umar dan Hafsu dan Ghiyas ya ce: “Babana ya ba mu labari ya ce, A’amashi ya ba mu labari ya ce, Ibrahim ya ba ni labari daga Aswad daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Wata rana muna tare da Manzon Allah (SAW) a wani kwarin (kogon) Mina, lokacin da aka saukar masa suratul Mursalati kuma lallai shi (Annabi) yana karanta ta, kuma ni ina koyonta daga bakinsa, lokacin bakinsa na da sauran danyantaka (sabonta) da ita. Sai wata macijiya ta tuma gare mu. Annabi (SAW) ya ce, “Ku kashe ta”, sai muka yi sauri kanta sai ta gudu. Sai Annabi (SAW) ya ce, “An tserar (kubutar) da ita daga sharrinku, kamar yadda aka tsare ku daga sharrinta.”

306. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga dan Shihab daga Urwata dan Zubair daga A’isha matar Annabi (SAW) (Allah Ya yarda da ita), cewa: Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, game da hukuncin tsaka, (ya ce) fasika ce. Amma ban ji shi ya yi umarni da kashe ta ba.”

Babi na Takwas:
Ba a cire itacen Harami. dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: Daga Annabi (SAW) cewa: “Ba a cire kayarta (wanda bai kan hanya).”

307. An karbo daga kutaiba ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Sa’id dan Abu Sa’idul Makburi daga Abu Shuraih Al-adawi cewa: Lallai shi ya ce, ga Amru dan Sa’id lokacin da zai aika runduna zuwa Makka cewa: “Ka yi mini izini ya Sarkin Muminai in ba ka labarin wata magana da Manzon Allah (SAW) ya tsayu da ita a safiyar (ranar) Budi (Cin Makka da yaki). Kunnuwana sun ji shi kuma zuciyata ta kiyaye shi. Kuma idanuwana sun gan shi lokacin da ya yi magana da shi cewa: “Lallai shi (Annabi) ya yi wa Allah godiya ya yabe shi, sa’an nan ya ce: “Lallai Makka Allah Ya haramta ta ba mutane suka haramta ta ba. Saboda haka ba ta halatta ga kowane mutum da ya yi imani da Allah da Ranar Lahira (karshe) ya zubar da jini a cikinta ko ya tunbuke itaciyarta. Idan wani ya nemi ya saukaka (halatta) saboda yakin da Manzon Allah (SAW) ya yi da ita, to, ku ce masa: “Hakika Allah Ya yi izini ga ManzonSa (SAW) na dan karamin lokaci ne kadai. Amma ku ba a yi muku izini ba, Kuma lallai ni, an yi mini izini a bisa wata sa’a daya ce daga cikin yini kuma hakika haramcinta ya komo yau kamar yadda haramcinta yake a jiya. Wanda yake halarce ya isar ga wanda ba ya halarce.” Sai aka ce, wa Abu Shuraih cewa: “Me Amru ya fadi maka? Ya ce, “Ni na fi ka sanin haka ya Abu Shuraih, hakika harami ba shi ba da mafaka ga mai sabo, ko ga mai kisan kai, kuma ba mafakar barawo ba ne.”