✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama direban Sardauna a bikin shekara 50 da kafa Gidan Arewa

An karrama Alhaji Ali Sarkin Mota, direban marigayi Sardauna a bikin cika shekara 50 da kafa 'Arewa House'

A ci gaba da bikin cika shekara 50 da kafa Gidan Arewa da ke Kaduna, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya karrama, Alhaji Ali Sarkin Mota, mutumin da ya tuka Firimiyan Arewacin Najeriya, Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

Sarkin Musulmin ya bukaci shugabanni da manyan baki da suka halarci taron da su girmama Alhaji Ali Sarkin Mota.

Alhaji Ali Sarkin Mota na gaisawa da manyan baki a taron bikin shekara 50 da kafa gidan ‘Arewa House’.
Manyan baki sun mike domin girmama Alhaji Ali Sarkin Mota, direban Sardauna a lokacin taron bikin cikar ‘Arewa House’ shekara 50 da kafuwa.
Wani sashe da gwamnoni daga cikin manyan bakin da suka halarci taron.

Dattijon ya doddogara sandarsa ya zagaya wuraren da manyan baki das suka halarci taron.

Aminiya ta rawaito cewa, taron ya samu halartar gwamnoni gwamnonin jihohin Ekiti, Jigawa, Sokoto, Kebbi, Kaduna da sauransu sun halarci taron.

Sauran manyan bakin sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Muhammada Namadi Sambo, Ministan Muhalli, Mohammed Mahmud Abubakar ta takwaransa na Ma’aikatar Harkokin ‘Yan Sanda, Maigari Dingyadi; Ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Hussain Adamu da sauran manyan baki da dama.

Gwamnan Jihar Ekiti kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi shi ne babban bako mai jawabi a wurin taron.