✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama Sarkin Hayin Malam Bello kan zaman lafiya

Hukumar Samar da zaman Lafiya a Tsakanin Al’ummar Jihar Kaduna ta karrama Sarkin Hayin Malam Bello da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, Alhaj…

Hukumar Samar da zaman Lafiya a Tsakanin Al’ummar Jihar Kaduna ta karrama Sarkin Hayin Malam Bello da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, Alhaj Kabiru Isa Gangarida saboda gudunmawar da yake bayarwa wajen samar da zaman lafiya a yankin.

A lokacin da yake karbar takardar yabo bisa kokarin da yake yi wajen inganta zaman lafiya da samar da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummar yankin, Alhaji Kabiru Isa Gangarida ya gode wa  hukumar kan  karrama shi.

Ya kara da cewa zai ci gaba da taka rawa wajen ganin an tabbatar da jama’ar unguwar sun kasance cikin zaman lafiya a kowane lokaci.

“Ina matukar farin ciki da zuwanku domin karrama ni bisa kokarin da muke yi wajen samar da fahimta da zaman lafiya a tsakanin mazauna wannan yanki namu na Hayin Malam Bello. Wannan karramawar da kuka yi mana mun yi farin ciki da ita domin ya nuna kun yaba da kokarin da muke yi, kuma za mu kara,” inji shi.

Ya bayyana cewa zaman lafiya shi ke kawo ci gaba a cikin al’umma don haka zai ci gaba da ba da tasa gudunmawar domin samun ci gaban Hayin Malam Bello. Sai ya yaba wa hukumar bisa kokarin da take yi wajen tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kaduna.