✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama Shah Rukh Khan da Ban Damme da Jackie Chan a Saudiyya

A wani bikin karramawa ba a cika ganin irinsa ba, kasar Saudiyya ta karrama fitattun jarumin fina-finan Indiya Shah Rukh Khan da takwaransa na Amurka…

A wani bikin karramawa ba a cika ganin irinsa ba, kasar Saudiyya ta karrama fitattun jarumin fina-finan Indiya Shah Rukh Khan da takwaransa na Amurka Ban damme a wani gagarumin biki karrama ’yan fim da aka yi a kasar.

A bikin, an karrama jaruman fina-finai daga kasashen duniya 15, kuma an ba su lambar yabo ta Joy Edcellence Award ne. Shah Rukh Khan ya wallafa sakon godiyarsa ga Saudiyya a shafinsa na Tiwita tare da sanya hotunan yadda bikin ya gudana.

Da ya zo jawabin godiya yayin karramawar, jarumin ya fara ne da karanta Bismillah. Shi dai Sha Rukh Khan Musulmi ne, amma matarsa Gauri Khan mai bin addinin Hindu ce kuma sun shafe shekara 28 suna tare.

King Khan kamar yadda aka fi saninsa da shi ya yi magana a kan ci gaban da Saudiyya za ta samu nan gaba lura da yadda ta bude gidajen kallon sinima, bayan da Yarima mai jiran gado ya dage haramcin da da aka sanya a da.

Ya kara da cewa “Insha Allah, za mu kasance cike da doki saboda an bude gidajen kallo a nan Saudiyya. Akwai labarai da dama da za a fada, kuma mu a matsayinmu za mu taimaka da duk abin da za mu iya.”

Sauran wadanda aka karrama sun hada da wata fitacciyar jarumar kasar Masar Ragaa El Gedawy da jarumin Game of Thrones da Akuaman Jason Momoa. Jason Momoa ya ce ya fada cikin kaunar Saudiyya dumu-dumu tun karon farko da ya je kasar a shekarar 2017.

Ya kara bayani kan yadda ya taka rawa a sauyin da aka samu a Saudiyya: “Abu ne mai kyau a ga sauyin da aka samu ko don al’umma mai tasowa,” inji shi.

Jarumi dan asalin Beljiyum Jean-Claude Ban Damme da aka karrama ya ce ya ji dadi da aka ba shi lambar yabo mai siffar mikiya mai ruwan gwal.

Baya ga wadannan akwai kuma fitaccen jarumin fina-finai dan kasar Hong Kong wato Jackie Chan da shi ma ya karbi lambar karramar, sannan da hawansa kan dandamali sai ya ce “Salam alaikum.” Kamar yadda BBC ya ruwaito.

“Na san da yawanku sun san ni. Na shafe shekara 59 ina yin fim. Wannan ne karo na farko da na zo Saudiyya, gaskiya babbar kasa ce. Ina fata in sake dawowa da tawagata ta shirya fim nan kusa,” inji shi.