✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama Sheikh Ahmad Lemu da lambar yabo ta Sarki Faisal a Saudiyya

Muhimman mutane biyar ne suka samu lambar yabo ta Sarki Faisal a wannan shekarar, wadanda suka hada da dan Najeriya, kuma malamin addinin Musulunci, Sheikh…

Muhimman mutane biyar ne suka samu lambar yabo ta Sarki Faisal a wannan shekarar, wadanda suka hada da dan Najeriya, kuma malamin addinin Musulunci, Sheikh Dokta Ahmed Abubakar Lemu. Wannan lambar yabo ta Sarki Faisal, kasar Saudiyya kan bayar da ita ne ga mashahuran mutanen da suka yi fice a duniya, inda a bana aka bayar da ita  fannin kimiyya ga mashahurin masanin lissafi, Farfesa Gerd Falting na kasar Jamus; a fannin magani kuwa a bayar da ita ne ga Farfesa Yuk Ming Dennis Lo dan kasar Sin.
A fannin Harshen Larabci da adabi, an bayar da lambar yabo ta Sarki Faisal ga Dokta Abdullah Ibrahim Allawi Albussabah na kasar Iraki. An fannin darussan addinin Musulunci kuwa, an bayar da lambar ne ga Farfesa AbdulWahab Ibrahim Abou Sulaiman, daya daga cikin ’yan maajlisar manyan malaman addinin Musulunci ta Masarutar Saudiyya.
Sheikh Dokta Ahmad Abubakar Lemu dan Najeriya, an ba shi wannan lambar ne saboda la’akari da aka yi kan irin gudunmuwar da ya yi a ayyukan addinin Musulunci. Sannan shi ne dan Najeriya na biyu da ya samu wannan lambart yabon, bayan Marigayi Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi da aka karrama shekarar 1987.