✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Buhu ta Filato

Wata kungiyar matasa mai suna IEYAN reshen Jihar Filato ta karrama wadansu manyan mutane su 11 da ta ce sun bayar da gudunmawa, a bangarori…

Wata kungiyar matasa mai suna IEYAN reshen Jihar Filato ta karrama wadansu manyan mutane su 11 da ta ce sun bayar da gudunmawa, a bangarori da dama na taimaka wa al’umma a Jihar Filato.

Kungiyar ta gudanar da taron karramawar ce, a ranar Lahadin da ta gabata a garin Jos, babban birnin Jihar Filato.

Mutanen da aka karrama  sun hada da Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Buhuna ta Jihar Filato Alhaji Iliyasu Muhammad da Daraktan Ayyuka na Karamar Hukumar Jos ta Kudu, Mista Daniel Bot  da Alhaji Nafi’u Barikin Ladi da tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta Karamar Hukumar Jos ta Arewa Alhaji Yaro Mai Rake da Mista Luka Panpe da sauransu.

Da yake jawabi a wajen bikin Shugaban Kungiyar IELAN reshen Jihar Filato, Kwamared Ajiya  Wuddeama ya  ce sun karrama wadannan mutum 11 ne, kan irin gudunmawar da suke bayarwa wajen taimakawa al’ummar Jihar Filato a bangarori daban-daban domin  karfafa musu gwiwa.

Ya ce kamar Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Buhu ta Jihar Filato Alhaji Iliyasu Muhammad sun karrama shi ne   saboda taimaka wa matasa  da yake yi, wajen samar musu da  ayyuka a gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Ya ce ya samar wa matasa da dama  aikin  dan sanda da aikin shige da fice da aikin Kwastam da kuma samar wa matasa ayyuka a  wurare daban-daban a jihar.

Ya ce a shirye kungiyar take ta ci gaba da zakulo irin wadannan mutane da suke taimaka wa al’umma domin ta karfafa musu gwiwa.

Ya yi kira ga jama’a musamman masu hannu da shuni su rika taimaka wa al’umma.

A jawabin Alhaji Iliyasu Muhammad ya bayyana matukar farin cikinsa da  karramawar da wannan kungiya ta yi musu.

“Muna yin wannan aiki ne don Allah ba tare da kowa  ya sani ba.

Amma Allah  Ya sanar da wannan kungiya cewa ga hidamar da muke yi wa al’umma. Babu shakka duk wanda yake ayyukan alheri, aka nuna an ji dadi zai yi farin ciki, kuma  zai samu karfin gwiwa, wajen ci gaba da wadannan ayyuka,” inji shi.