✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama ’yan fim bangaren Kwankwasiyya

A ranar Asabar da ta gabata ce aka gudanar da bikin karrama ’yan fim wadanda suka tallata bangaren Kwankwasiyya da Jam’iyyar PDP a zabubbukan da…

A ranar Asabar da ta gabata ce aka gudanar da bikin karrama ’yan fim wadanda suka tallata bangaren Kwankwasiyya da Jam’iyyar PDP a zabubbukan da suka gabata, musamman a Jihar Kano.

Taron wanda ya gudana a dakin taro na Yazeed Royal Suite da ke kan Titin Sakkwato a Kaduna ya samu halartar Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda shi ne shugaban taron da sauran manyan ’yan Kwankwasiyya na Kano da Kaduna da sauransu.

Daga cikin jaruman Kannywood da aka karrama akwai Sani Danja da Yakubu Muhammed da Mustapha Naburaska da Abba Elmustapha da Ali Artwork da Sadik Zazzabi da Aminu Ala da Abubakar Sani.

Sauran sun hada da Darakta Sunusi Oscar 442 da jarumi Garzali Miko da Hadiza Kabara da Naziru Sarkin Waka da Tijjani Gandu da sauransu.

A sakonsa ga wadanda aka karrama, dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Abba Kabir Yusuf ya mika godiyansa ga masu nishadantarwar bisa yadda suka jajirce wajen tallata Kwankwasiyya.

“Ina taya ku murnar samun wannan kyauta ta karramawa daga Kwankwasiyya Reporters, wadda aka ba ku domin jin dadin yadda kuka jajirce wajen yada akidar Kwankwasiyya a Najeriya,” inji shi.

Sai ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da taimakonsu a harkokinsu baki daya.

Jarumi Naburaska lokacin da yake karvar kyautarsa
Jarumi Naburaska lokacin da yake karvar kyautarsa

A jawabin godiya, Jarumi kuma Darakta Sani Danja cewa ya yi, “Muna godiya ga Allah domin a Kano mun yi nasara. Duk abin da kake yi idan kana kan gaskiya, ko ka yi nasara ko ka fadi wallahi ka yi nasara. Saboda har yanzu mu ne muke zagayawa hankali kwance ba tare waige-waige ba. Saboda ka san ba a hada baki da kai an cuci wani ba. Muna godiya ga Kwankwasiyya Reporters, muna addu’ar Allah Ya kara daukaka.

“Sannan a madadin abokan sana’ata, ina kira gare ku duk labarin da za ku bayar ya zama na gaskiya. Babu kari, duk abin da za mu yi ya kasance cikin gaskiya.

A jawabin jarumin barkwanci Mustapha Naburaska ya bayyana cewa da Allah suka dogara, “Ko mun ci ko ba mu ci ba, Allah Ya ciyar da mu. Mun kayar da marasa daraja. Don haka gudunmawar da Kwankwasiyya Reporters ke bayarwa ga wannan tafiya, muna murna.”