✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe dan sanda tare da sace Bature a Bebeji

Masu garkuwa da mutane sun sace daya daga cikin Injiniyoyin Kamfanin Julius Berger dan kasar waje da ke aikin hanyar Kano zuwa Kaduna a garin…

Masu garkuwa da mutane sun sace daya daga cikin Injiniyoyin Kamfanin Julius Berger dan kasar waje da ke aikin hanyar Kano zuwa Kaduna a garin Bebeji tare da kashe dan sandan kwantar da tarzoma wadda ke aiki tare da su, mai suna Saje Bulus Adamu.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe takwas na safe a garin Bebeji ta Jahar Kano. Majiyar Aminiya ta bayyana cewa gawar dan sanda da aka kashe an kawo ta asibitin koyarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma ta kara da cewa an fara magana da masu garkuwa da Baturen a ranar Lahadi domin biyan kudin fansar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Jami’in hulda da jama’a na rudunar ‘yan sandan Jahar Kano, SP Magaji Musa Majiya ya ce tabbas an sace wannan Injiniya kuma dan sanda daya ya rasa ransa.

Kuma ya kara da cewa a halin da suke ciki yanzu haka sun hada gwiwa da rundunar  ‘yan sandan jahohin Kaduna da Katsina da kuma Zamfara don ceto wannan Injiniya ba tare da an cutar da shi ba.