Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An kashe fararen hula 7000 bara a kasar Siriya

Rahotannin sun nuna cewa akalla mutum dubu 6,964 aka kashe a kasar Syria sakamakon hare-haren da ake kai wa juna tsakanin gwamnatin Shugaban Kasar Bashar Al-Assad da sauran bangarorin ’yan tawaye.

Hukumar Kare Hakkokin dan Adam ta Siriya (SNHR) ce ta fitar da wani rahoto da ke bayyana adadin mutanen da aka kashe a bara a kasar. Rahoton ya nuna cewa an kashe fararen hula dubu 6,964 da suka hada da yara kanana dubu 1,436 da mata dubu 1,361.

ADVERTISEMENT

Rahoton ya kara da cewa gwamnatin Siriya tana da alhakin kashe fararen hula dubu 4,162 da suka hada da yara kanana 713 da mata 799.

Dakarun Rasha da ke taimaka wa Siriya da hare-hare ta sama kuma ke da alhakin kashe fararen hula 467 da suka hada da yara kanana 169 da mata 118.

ADVERTISEMENT

Dakarun Amurka kuma sun kashe fararen hular Siriya 417 da suka hada da yara kanana 175 da mata 118.

Rahoton ya kuma ce, akwai kuma fararen hula dubu 1,107 da ba a san wa ya kashe su ba wadanda su ma suka hada da yara kanana 247 da mata 216.

’Yan ta’addan Daesh kuma a 2018 sun kashe fararen hula 446 da suka hada da yara kanana 82 da mata 56 a Siriya.

Rahoton ya bayyana cewa, ’yan ta’addan ’yan aware na PKK/YPG sun kashe fararen hula 285 da suka hada da yara kanana 29 da mata 39.

Hukumar ta SNHR ta kuma bayyana cewa akwai mutum 976 da aka kashe saboda zalunci wanda kashi 97 gwamnatin Siriya ce take da alhaki.

Rahotan ya kuma ce gwamnatin Siriya ta zalunta tare da kashe mutum 951 a yankunan kasar daban-daban.

An bayyana cewa, a dai wannan lokaci ’yan ta’addan YPG/PKK sun kashe mutum 10 ta hanyar zaluntarsu, sannan ’yan ta’addan Daesh sun kashe mace daya ta hanyar zaluntarta kamar yadda TRT ta ruwaito.

 

…Za mu jagoranci sulhu a  Syriya – Jamus da Rasha

Domin samar da zaman lafiya da lumana a kasar Siriya, Shugabar Jamus Angela Merkel ta gana da Shugaban Rasha Bladimir Putin inda suka tattauna kuma suka fahimci juna a kan bin hanyar siyasa domin kawo karshen rikicin kasar Siriya da ya dade ana kwan-gaba-kwan-baya.

A wata sanarwa da Mataimakiyar Mai magana da yawun gwamnatin Jamus, Ulrike Demmer ta fitar ta bayyana cewa a ganawar, Shugaban Rasha Putin da Shuagabar Jamus Merkel sun tabo batutuwan kasa da kasa da kuma lamuran kasar Siriya da Ukraine.

Demmer ta bayyana cewa abubuwan da suka kasance a kan gaba lokacin tattaunawar shugabannin biyu sun hada da kafa kwamitin samar da kundin tsarin mulki a Siriya da kuma janye sojojin Amurka daga Siriya.

Dukan bangarorin biyu sun aminta a kan bin hanyar siyasa a matsayin hanyar da ta fi dacewa domin warware rikicin Siriya.

Demmer ta bayyana cewa Shugaba Merkel ta bayyana farin cikinta akan taron tsagaita wuta da aka gudanar a ranar 27 ga watan Disamba a Ukraine.