Da Dumi Dumi

An kashe masu zanga-zanga 106 a Iran – Kungiyar Amnesty

Gwamman mutane ne ake fargabar sun mutu a kasar Iran tun bayan barkewar zanga-zanga kan karin kudin man fetur Juma’ar makon jiya, in ji ofishin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya.

Mai magana da yawun ofishin ya nemi jami’an tsaro da su daina amfani da karfi fiye da kima da ya hada da amfani da harsashi. Ya kuma yi kira da gwamnatin Iran ta dawo wa da ’yan kasar Intanet.

Kungiyar ta Amnesty International din ta ce ta samu sahihan rahotanni da ke nuna cewa akalla mutum 106 aka kashe a biranen kasar guda 21.

Gwamnatin Iran dai ta musanta cewa mutanen da suka hau tituna masu zanga-zanga ne.

Shugaba Rouhani ya ce “Duk wani dan kasa na da ’yancin yin zanga-zanga wadda ta banbanta da bore.”

ADVERTISEMENT

Har kawo yanzu dai babu cikakken bayani dangane da abin da ke faruwa saboda rufe intanet da aka yi ranar Asabar.

Tun dai a ranar Juma’ar makon jiya, masu zanga-zanga ke ci gaba da hawa tituna a biranen kasar domin nuna rashin amincewarsu kan karin farashin mai da gwamnati ta sanar za ta yi da kaso 50%.

A ranar Lahadi ne zanga-zangar ta fadada zuwa birane da garuruwa 100, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Fars News ya sanar.

Akalla masu zanga-zangar sun kona bankuna 100 da shaguna 57 sannan an kama fiye da mutum dubu daya.

Shugaba Hassan Rouhani ya ce gwamnati ta yi karin ne domin samar da kudaden da za a bai wa ’yan kasa mabukata. Jerin takunkuman da Amurka ta kakaba wa ne dai suka jefa Iran cikin wannan yanayi. Kamar yadda kafar BBC ta ruwaito.

Masu bore sun kashe jami’an tsaro

Masu boren sun kashe jami’an tsaron kasar uku ta hanyar daba musu wuka a yammacin birnin Tehran.

An tabbatar da mutane biyar suka mutu yayin zanga-zangar da ta barke a wasu biranen kasar.

Shugaba Hassan Rouhani, ya kafe cewa karin farashin man fetur din zai taimakawa kasar samun karin kudaden shigar da adadinsu ya kai dala biliyan biyu da miliyan 55 a shekara, kwatankwacin kudin kasar Riyal tiriliyan 300.

Matakin kara farashin man a Iran ya zo ne kwanaki kalilan bayan sanar da gano arzikin gangar danyen mai akalla ganga biliyan 53 kwance a wani fili da ke kudancin kasar.

Yanzu haka dai Iran na kan fama da takunkuman karya tattalin arzikin da shugaba Donald Trump ya kakaba mata, bayan janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da Iran din ta cimma da manyan kasashen Turai a shekarar 2015.

Yadda zanga-zangar ta faro

Zanga-zanga ta barke ne a ranar 15 ga watan Nuwamban da muke ciki, bayan da gwamnati ta kara farashin man fetur da kimanin kashi 50 cikin 100.

Farashin man fetur ya tashi a daukacin Iran da kashi 50 bayan da aka janye tallafin man.

Dalilin yin haka a cewar gwamnati shine don ta samu kudin da za ta tallafawa marasa karfi.

Dama Iran na fama da gurguncewar tattalin arziki saboda takunkumin da Amurka ta kakaba mata tun bayan da kasashen biyu su ka yi baram-baram kan shirin nukiliyar Iran.

Mutune biyu sun rasa rayukansu a garuruwan Sirjan da Behbahan kuma gwammai sun jikkata.

Kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa an yi arangama da jami’an tsaro a lokacin da masu zanga zangar suka yi yunkurin kona wata ma’ajiyar man fetur a ranar Juma’a.

Wasu garuruwan da rikicin ya shafa sun hada da babban birnin kasar wato Tehran da Kermanshah da Isfahan da Tabriz da Karadj da Shiraz da Yazd da Boushehr da kuma Sari. A yawancin biranen masu boren sun rufe hanyoyi ta yin amfani da ababen hawansu don rufe hanya.

Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a internet sun nuna wasu gine gine na ci da wuta da suka hada da bankuna.

Shugaba Hassan Rouhani ya bayyana cewa kashi 75 na ’yan kasar na cikin matsi, kuma karin farashin zai tafi ne kacokan kan tallafa musu don ganin sun samu saukin rayuwa. Iran na daga cikin kasashen da ke samar da man fetur a duniya, kuma ta na sayar da man nata da sauki sosai.

To sai dai takunkumin da Amurka ta kakaba mata ya dagula al’amura a kasar, da suka hada da kasa samun damar shigo da injunan da mahakar man fetur din kasar ke bukata.

Har ila yau, tattalin arzikinta ya lalace, yayin da darajar kudinta ta yi kasa, dalilian da suka haifar da hauhawar farashin ababen more rayuwa.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya