✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe masu zanga-zanga a Sudan

Bayanai daga Sudan na cewa an kashe masu zanga-zanga uku da wani jami’in tsaro daya yayin wani artabu a Babban Birnin kasar, Khartoum. Majalisar Soji…

Bayanai daga Sudan na cewa an kashe masu zanga-zanga uku da wani jami’in tsaro daya yayin wani artabu a Babban Birnin kasar, Khartoum.

Majalisar Soji da ke jagorantar kasar tun bayan hambarar da Shugaba Omar Al-Bashir a watan jiya ta ce an jikkata masu zanga-zanga da dama.

Rahotanni sun nuna cewa an samu ci gaba a tattaunawa tsakanin sojoji da wata gamayyar ’yan adawa wajen kafa hukumar da za ta jagoranci kasar.

Daya daga cikin masu zanga-zangar a Khartoum Lina Hieba ta shaidawa BBC cewa “wasu mutane a kayan sojoji” sun harba musu harsashi.

Sannan ta bayyana lamarin a matsayin wani “gagarumin arangama”, inda ta ce an kashe wasu masu zanga-zangar yayin da aka tafi da wasu asibitoci.

Hakanan kuma ta yi watsi da kalaman Majalisar Soji da ke cewa wasu da ba a san ko su waye ba ne suka harbi masu zanga-zanga, inda ta ce wani yunkuri ne na karkatar da tattaunawar da ake yi tsakanin shugabannin zanga-zangar da sojoji.

“Ba mu yarda da haka ba kuma ba mu amince da su ba,” a cewar Heiba.

A baya dai babban mai shigar da kara na kasar ya ce an tuhumi Mista Bashir da wasu mutane bisa kisan masu zanga-zangar.