✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe masu zanga-zanga biyar a Bagadaza

A kalla mutum biyar jami’an tsaron Iraki suka harbe bayan da suka yi amfani da harsashin gaske a kan masu zanga-zanga a Bagadaza, a cewar ’yan…

A kalla mutum biyar jami’an tsaron Iraki suka harbe bayan da suka yi amfani da harsashin gaske a kan masu zanga-zanga a Bagadaza, a cewar ’yan sanda da jami’an asibiti.

Jami’an tsaro sun yi harbe-harbe ne a kan masu zanga-zangar wadanda suka kusanci ofishin Firayi Minista da tazarar mita 500.

A baya, jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashin roba domin hana masu zanga-zangar da suka yi kokarin keta shingayen da aka dasa a tsakaninsu da ofishin Firayi Ministan.

Ya zuwa yanzu dai akalla mutum 250 aka kashe tun da aka fara zanga-zangar adawa da gwamnati a farkon watan Oktoban bana a kasar ta Iraki.