✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutane 1,891 a rikicin Filato

Kwamitin mutum bakwai da Gwamnatin Jihar Filato ta kafa, don sake dawo da ‘yan gudun hijirar jihar zuwa garuruwansu, ya bayyana cewa ya gano mutane…

Kwamitin mutum bakwai da Gwamnatin Jihar Filato ta kafa, don sake dawo da ‘yan gudun hijirar jihar zuwa garuruwansu, ya bayyana cewa ya gano mutane 1,891 ne suka rasa rayukansu a rikice-rikicen da aka yi a Kananan Hukumomin Jos ta Arewa da Bassa da Riyom da Barikin Ladi da Bokkos da ke jihar.

Shugaban Kwamitin, Eya Bayis Mashal Bala Danbaba ne ya bayyana haka, a lokacin da yake mikawa Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong rahoton kwamitin a gidan Gwamnatin jihar da ke Jos a tsakiyar wannan makon.

Kwamitin wadda Gwamnatin Jihar Filato ta kafa a Watan Yulin da ya gabata ya ce ya gano cewa mutane dubu 50 da 212 ne suka yi gudun hijira, daga ainihin wuraren da suke zaune a cikin al’ummomi 118 da wuraren da al’ummar Fulani suke zaune guda 98 zuwa wasu wurare daban-daban, sakamakon wadannan rikice-rikice.

Har’ila yau kwamitin ya ce ya ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijirar da rikice-rikice 27 suka tarwatsa, tare da karbar takardun bayanai guda 55 daga al’ummomi da sauran mutanen da rikice-rikicen suka shafa.

Haka kuma kwamitin ya ce ya gano cewa an lalata kauyuka guda 78 tare da lalata gonaki da kayayyakin amfanin gona a wadannan wurare da rikici-rikicen suka shafa. Sai kuma ya ba gwamnati shawarar ta dawo da mutanen da suka yi gudun hijirar a duk lokacin ta fahimci cewa harkokin tsaro sun kyautatu a wadannan wurare.

Hakazalika kwamitin ya shawarci gwamnati ta tanadar wa ’yan gudun hijirar da suke son komawa garuruwansu na asali, kayayyakin da zasu sake gina muhallansu da aka lalata a lokacin rikice-rikicen.

Da yake jawabi lokacin da yake karbar rahoton, Gwamna Lalong ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta yi nazarin rahoton kwamitin tare da aiwatar da shawarwarin ba tare da bata lokaci ba. Sannan ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da zaman lafiya kuma su guji yada jita-jita.