✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutane da dama a Kananan hukumomi 3 a Katsina

A wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kai unguwannin kananan hukumomin: Dan Musa, Faskari da Batsari a jihar Katsina. Rahotanni da dama sun bayyanawa…

A wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kai unguwannin kananan hukumomin: Dan Musa, Faskari da Batsari a jihar Katsina.

Rahotanni da dama sun bayyanawa majiyarmu cewa, ‘yan bindigar sun kai harin ne akan babura inda  suka dinga kashe duk wanda suka samu.

A yankin Sabon Layin Galadima da ke karamar hukumar Faskari sun kashe akalla mutum 11.

Sai dai kakakin hukumar ‘yan sandan jihar SP Gambo Isah ya ce, mutum daya aka harba kuma yana asibiti ana yi masa jinya.