Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An kashe mutane da yawa tare da kone gidaje 50 a Taraba

Wasu fusatattun kabilar tibi da ake zargin sun kai hari garin Sondi, a birnin kabilar Jukun da ke Karamar Hukumar Wukari a jihar Taraba, inda suka kashe mutane da yawa tare da kone kimanin gidaje 50 a karshen makon.

An samu rahoton kona masarautar Chunko da ofishin ‘yan sandan garin wanda ake zargin maharan ne suka aikata hakan a garin Chunko.

ADVERTISEMENT

Shugaban kungiyar matasan Jukun Zando Hoku, ya bayyanawa majiyar mu cewa, an kashe mutum bakwai daga cikin wadanda suka harin. Sai dai shugaban Kungiyar kabilar Tibi na jihar ya ce, wannan harin ramuwar gayyace, saboda akwai lokacin da kabilar Jukun suka harbe wani mutum da iyalin shi a garin Joita da ke da iyaka tsakanin Jihar Benuwe da Taraba.

ADVERTISEMENT