Da Dumi Dumi

An kashe mutum 1 da yin garkuwa da 4 a kauyen Kaduna

Rahotanni na bayyana cewa a kashe wani mutum mai suna Mista Ezra Haruna, tare da yin garkuwa da mutuum 4 a Safiyar ranar Litinin a Anguwan Barau, cikin garin Udawa, Karamar Hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an yi garkuwa da mutum 4 Anguwan Barau lokacin da ‘yan bindiga suka shiga garin da misalin karfe 4:00 na asubahi.

A lokacin da ‘yan bindigar suka fara harbi sai jama’ar garin suka rika gudu ko ina hakan yasa daya daga cikin su ya mutu.

Wadanda aka yi garkuwan da su sun hada da: Misis Jummai Ido, matar a cocin Godiya Baptist Church, Angwan Barau Udawa; Mista Luka Auta, Mista Sale Auta da Mista Yakubu Audu.

ADVERTISEMENT
Share