✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 2 da tarwatsa sansanin masu garkuwa a Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kashe mutum biyu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne tare da tarwatsa maboyar masu garkuwa da mutane…

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kashe mutum biyu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne tare da tarwatsa maboyar masu garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Alkaleri da ke Jihar.

Jami’an sun yi hakan ne bayan sa’o’i 48 da kashe wani dan fashi da makami a wani samame da suka kai kauyen Miri cikin karamar Hukumar Bauchi.

Jami’in hulda da jama’a na Hukumar ‘yan sandan jihar DSP Kamal Datti Abubakar, ne ya sanar da hakan a Bauchi, ya kuma ce jami’an ‘yan sandan sun kwato makamai da dama a samamen da suka kai maboyar.