Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An kashe mutum 3 a karamar hukumar Jama’a Kaduna

Akalla mutum uku ne aka kashe a sabon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a yammacin jiya Lahadi a Unguwar Asso da gadar Tanda a yankin gundumar Gwong karamar hukumar Jama’a jihar Kaduna.

Shugaban karamar hukumar Mista Peter Averik ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin labarai (NAN) hakan inda ya ce, ‘yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 7:30 PM na daren jiya yayin da suka fara budewa jama’ar yankin wuta tare da kashe wasu da kuma raunata wasu.

ADVERTISEMENT

A yanzu haka dai haka wadanada suka samu raunuka na asibitin Fadan Kagoma don yi masu jinya, a yau an samu rahoton daya daga cikin wadanda aka kai asibitin ya rasu.

ADVERTISEMENT