Da Dumi Dumi

An kashe mutum 3 a sabon hari a karamar hukumar Jama’a

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai a kauyen Gerti da gundumar Kaninkon da ke karamar hukumar Jama’a ta jihar Kaduna a safiyar jiya Litinin din nan.

Yayin da ya ke karin bayani ta wayar tarho, Kansilan Kaninkon, Christopher Yakubu Phillip ya ce lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 8:00 na safe, ya shafi wani mutum ne tare da dansa yayin da suke aiki a gonarsu.

Phillip, ya ce mutum na hudu da ya sha da qyar ne ya kawo labarin inda suka umurci ragowar manoman da su baro gonakinsu inda aka sanarwa sa jami’an tsaro na sojoji da suka jagoranci shiga dajin inda aka gano gawarwakin waxanda aka kashe.

Kansilan ya bayyana harin a matsayin abin takaici musamman a daidai wannan lokacin da manoma ke shirye-shiryen noma a gonakinsu, inda yayi kira ga jami’an tsaro da su yi duk abinda ya kamata don kamo marasa son zaman lafiya a yankin.

Sannan a karshe ya roki gwamnati da ta kara tsaurara tsaro a yankin don zakulo marasa kishin da ke aikata haka wanda rashin hakan ka iya raunata aikin harkar noma a yankin.

ADVERTISEMENT

Wani mutumin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa Aminiya cewa, suna zaune a gida su ka jiyo karar bindigi inda wasu suka ce masa su shiga don tabbatar da abin da ke faruwa, amma ya shaida musu cewa me zai kai shi cikin daji shi ba jami’in tsaro ba, “to daga baya sai mu ka ji labarin maharan sun kashe mutum uku a gona.” Inji shi

Share