✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 4 a wani sabon hari a Kudancin Kaduna

An kashe mutum hudu tare da jikkata wasu hudu a wani harin kwanton bauna da aka kaiwa wasu matasa. Jim kadan da kammala wasan kwallon…

An kashe mutum hudu tare da jikkata wasu hudu a wani harin kwanton bauna da aka kaiwa wasu matasa. Jim kadan da kammala wasan kwallon kafa a kauyen Zunuruk da ke karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na yamma kamar yadda wani ganau ya shaidawa Aminiya ta wayar tarho, inda ya ce maharan sun kawo farmakin ne daidai an tashi wasan kwallon inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, inda nan take suka kashe mutum hudu, wasu hudu kuma suka samu mummunar rauni.

Wadanda aka kashe kamar yadda majiyar ta shaidawa Aminiya sun hada da; Cephas Peter mai shekara 39 da Solomon Yohanna mai shekara 48 da Felix John, mai shekara 46 da kuma Barnabas Garba mai shekara 37.