Da Dumi Dumi

An kashe mutum biyar a wani sabon hari a Kudancin Kaduna

Mutum biyar ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da aka kona gidaje da dama a wani hari da ’yan bindiga suka kai kauyen Zangan da ke Masarautar Attakar a Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna da ke iyaka da Karamar Hukumar Riyom a Jihar Filato.

Yayin da yake tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Jma’a, Shugaban Karamar Hukumar Kaura Mista Bege Katuka, ya ce maharan sun mamaye kauyen ne da misalin karfe 4:00 na yamma ranar Alhamis inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi.

“Mutum biyar ne suka mutu yayin da wadansu mutum biyu kuma suka bace. Sannan sun kona gidaje da dama ciki, har da karamin ofishin ’yan sanda da aka samar a yankin,” inji shi

Shugaban ya yi kira ga mutanen yankin su kai hankalinsu nesa domin jami’an tsaro na ci gaba da kokarin  samar da tsaro a wurin kuma suna ci gaba da gudanar da bincike don zakulo wadanda suka kai harin.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya musanta kona ofishin ’yan sandan.

ADVERTISEMENT

Ya ce bayan samun labarin Eriya Kwamanda na ’yan sandan Kafanchan ya jagoranci kai dauki inda maharan suka gudu zuwa saman dutsen da ke kusa da Karamar Hukumar Riyom a Jihar Filato.

“Binciken da muka fara ya nuna maharan sun shigo ne ta Jihar Filato, amma muna ci gaba da bincike.”

A takardar da Kungiyar Matasan Kaura (Kaura Youth Coalition) da Shugabanta na Kasa Kwamared Derek Christopher ya sanya wa hannu, ya ce daruruwan mahara suka keto kan iyaka suka kona gidaje 36 da cocin Katolika na St Peter da kuma cocin Anglican tare da kashe mutum bakwai.

Sun yaba wa Shugaban Karamar Hukuma, Katuka Bege Ayuba bisa damuwa da kokarin da ya yi bayan faruwar lamarin, sannan suka yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da tarayya da kungiyoyin addini da na farar hula su taimaka wajen kai musu  kayayyakin jinkai a sansanonin gudun hijirar da jama’arsu ke zaune tunda komai ya lafa.

Share