✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum biyu a Adamawa

Wasu ’yan bindiga sun kai hari kauyen Holma da ke Karamar Hukumar Hong da ke Jihar Adamawa, a Lahadin da ta gabata, inda suka kashe…

Wasu ’yan bindiga sun kai hari kauyen Holma da ke Karamar Hukumar Hong da ke Jihar Adamawa, a Lahadin da ta gabata, inda suka kashe mutum biyu tare da raunata mutum daya.

Mazauna kauyen sun ce ’yan bindigar sun kona gidaje fiye da ashirin da abinci.

Shugaban Rikon na Karamar Hukumar Hong, Usman Waganda ya kai ziyara wajen tare da jajantawa mutanen game da wannan hari da aka kai musu.

Ya ce an sanya matakan tsaro domin gano wadanda suka kai wannan hari tare da hukuntasu.

Ya kara da cewa za a kawo musu kayan masarufi domin samar musu saukin rayuwa bayan rashin da suka yi.

Mai Jamillan kauyen Hong, Micheal Wayamomni ya ce ’yan bindigan dai sun kai harin ne da misalin karfe 11 na daren Lahadi inda suka kona gidaje.

Ya tabbatar da mutuwar mutum biyu tare da daya da ya ji rauni sannan kuma shanu hudu sun bata.

Ya roki matakan tsaro da gwamnati dasu kara zage dantse wajen kulawa da rayukan mutane.

Kakakin ’yan sandan Jihar Adamawa, Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar harin.

Ya kara da cewa sun sanya a yi bincike kuma suna shugaban sashe na yankin wato DPO na Hong.

Ya ce wannan shi ne karo na uku da ’yan bindiga suke kai hari kauyen Holma sannan ya ce kai kara bayani bayan sun samu karin haske daga ofishinsu na can.