✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum hudu da kona gidaje a kauyen Kikon

Rikicin Fulani makiyaya da manoma ya barke a wata sabuwar fada da ake ganin mai da martani ne game da  kisan da ‘yan kabilar bachama…

Rikicin Fulani makiyaya da manoma ya barke a wata sabuwar fada da ake ganin mai da martani ne game da  kisan da ‘yan kabilar bachama da ake zargin sun yi wa Fulani  a watan da ya gabata  a kauyen Kikon da ke karamar hukumar Numan ta jahar Adamawa, inda mutum hudu suka rasa rayukansu sannan aka kona gidaje.

Rohutanni sun nuna cewa mutanen kauyen suna barci ne sai suka fara jin harbe-harbe, wadda ya tada su daga barci, da yawa daga cikin mutanen kauyen suka shiga daji domin su tsira. Bayan wannan harin sai ‘yan kabilar bachama suka  sake kai hari a kauyukan Dowayan-waja da Lure inda suka kashe duk abin da suka gani mai rai.

Shugaban karamar hukumar Numan, Mista Arnold Jibila ya tabbatar da faruwar rikicin ga manema labarai, sai dai ya ce ba zai iya fadin iya mutanen da suka rayukansu ba .

Sai dai wata majiya da ta nema a sakaya sunansu ta ce makiyayan sun shigo kauyen ne a Babura fiye da ashirin, sannan wasunsu kuma da kafa suka shigo, ganin hakan ya sanya mutanen kauyen suka buya a ciki daji.

Majiyar ta kara da cewa, mutum fiye da hudu sun rasa rayukansu, sannan mutane da dama sun ji raunuka, wadanda aka kai su asibitin da ke Numan.

“Idan ba a manta ba a harin farko da kabilar bachama ta fara kaiwa a kauyuka takwas inda suka kashe fiye da mutum sittin a kauyen Kikon. ‘’Ina ganin wannan harin da Fulani suka kai na da nasaba da harin farkon da bachama suka kai musu.”  Inji majiyar.

Kakakin ‘yan sanda na jahar Adamawa Othman Abubakar ya ce binciken da ‘yan sanda suka yi ya nuna cewa a kalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu a harin.  

Ya kara da cewa wadansu daga kauyen sun ji rauni amma an kaisu asibitin Numan, sannan gidaje da da dukiyoyi da dama sun salwanta a Kikon da kauyen Dowaya-waja.  

Ya ce ba su yi wata-wata ba suka tura ‘yan sanda kauyukan domin tabbatar da tsaro, sannan sun yi alkawarin kama duk wadanda aka samu da hannu a wannan harin.