✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe sojojin Amurka 2 a Afghanistan

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta fitar da sunayen sojoji biyu da aka kashe a wani harin harbi da ya auku a Gundumar Sherzad da ke Gabashin…

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta fitar da sunayen sojoji biyu da aka kashe a wani harin harbi da ya auku a Gundumar Sherzad da ke Gabashin Lardin Nangarhar na Afghanistan.

Sojojin sun hada da Saje Jabier Jaguar Gutierrez mai shekara 28 da Saje Antonio Rey Rodriguez shi ma mai shekara 28.

Wadansu sojoji shida kuma sun jikkata a lokacin da wani sojan kawance na Afghanistan ya bude wuta a kan dakarun Amurka da na Afghanistan da bindiga kirar Machine Gun, inji mai magana da yawun Rundunar Sojin Amurka a kasar.

Shah Mahmood, wanda shi ne Gwamnan Lardin Nangarhar, ya ce “Har yanzu ba a san ko sojan shigar burtu ya yi ba ko kuma lamarin ya faru ne bisa kuskure, ana dai ci gaba da gudanar da bincike.”

Wani jami’in Ma’aikatar Tsaron Afghanistan da aka sakaya sunansa saboda ba a ba shi izinin ya yi magana da kafafen labarai ba, ya ce maharin sojan Afghanistan ne ya kuma yi gardama da sojojin Amurka kafin ya bude musu wuta, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya ruwaito. Jami’in ya ce, sojan ba ya da wata alaka da Kungiyar Taliban.