Da Dumi Dumi

An kashe tsohon dan kwallon Afirka ta Kudu

Wadansu ’yan bindiga da ba  a san ko su wane ne ba sun kashe tsohon dan kwallon Afirka ta Kudu mai suna Marc Batchelor a ranar Litinin da ta wuce.

Kakakin ’Yan sandan kasar, Lungelo Dlamini ya ce maharan sun bude masa wuta ne lokacin da yake tafiya a motarsa da misalin karfe 6 na yammacin ranar Litinin a Johannesburg, babban birnin kasar.

Jami’in ya kara da cewa rundunarsa ba ta samu nasarar kama wani ko wadansu kan wannan aika-aika ba, amma suna tsananta bincike don zakulo su.

Marigayi Marc Batchelor ya yaba buga wa Kungiyar Kwallon Kafa ta Afirka ta Kudu Bafana-Bafana wasa, kuma yana kwallo ne a bangaren gaba. Baya ga haka ya buga wa kulob da dama a Afirka ta Kudu da suka hada da Kazier Chiefs Stars da kuma na Orlando Pirates.

Marigayi Batchelor yana daga cikin wadanda suke bayar da shaida a kotu game da tuhumar da ake yi wa Oscar Pistorius gurgun da ya lashe wa Afirka ta Kudu lambar Zinare a gasar Olamfik,  kuma ake zargi da kashe buduwarsa ta hanyar harbinta da bindiga, inda ya ce ya yi haka ne bisa kuskure.Fiye da shekara 5 ke nan da iyalan marigayiyar suka kai shi kara gaban kotu kuma har yanzu ana ci gaba da gudanar da shari’ar.

ADVERTISEMENT

Rahotanni sun ce Batchelor yana daga cikin wadanda suka bayar da shaida a kan halayyar tsananin fushi na Oscar Pistorious a wani zama da kotu ta yi a kwanakin baya.

Wadansu na zargin wannan na daga dalilin da ya sa aka kashe tsohon dan kwallon a wannan lokaci.

Share