Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An kashe wanda ake zargi da kitsa yunkurin juyin mulki a Habasha

Firay Ministan Habasha Abiy Ahmed
Firay Ministan Habasha Abiy Ahmed

Rundunar Sojin Habasha ta samu nasarar cafke wasu daga cikin wadanda ake zargi da yunkurin juyin mulki a yankin Arewacin kasar.

A daren Asabar ne wasu sojoji karkashin jagorancin Janar Asamnew Tsige suka yi yunkurin juyin mulkin a Amhara, daya daga cikin yanki 9 masu cin gashin kansu a Habasha, inda suka harbe shugaban yankin, Anabchew Mekonnen tare da wani mai ba shi shawara.

ADVERTISEMENT

Bara ne dai aka saki Janar Tsige daga gidan yari bayan shafe shekara 10 a daure, sakamakon yunkurin juyin mulki a kasar ta Habasha da ya jagoranta a shekarar 2009.

A ranar Litinin kuma kafofin watsa labaran gwamnatin kasar suka bada sanarwar cewa an kama kuma an kashe Birgediya Janaral Asaminew Tsige, a lardin Amhara. Jami’an tsaro sun ce an kashe shi ne yayin da yake kokarin ya gudu.

ADVERTISEMENT

Shi dai wannan hafsan sojan sannane ne a kasar Habasha musamman da yake ya taba rike mukamin Shugabancin Hukumar Tsaro ta yankin Amhara, kuma yana da goyon bayan dimbin ’yan kabilar Amhara din.

Tun kafin zuwa yanzu, Gwamantin Tarayyar kasar ta sha zarginsa da laifin kitsa rikice-rikicen da suka barkewa a yankin har aka kai ga hallaka shugaban yankin na Amhara.

Yankin Amhara shi ne na biyu mafi girma a Habasha bayan Oromo, yankunan da aka shafe shekara biyu ana zanga-zangar adawa da gwamnati da tilastawa tsohon Firay Minista Hailemariam Desalegn yin murabus.