Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An ki sako ’ya’yan Ardon Rijana duk da ya biya kudin fansa

Ardon Rijana da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a karamar Hukumar Kachiya da ke Jihar Kaduna Ardo Alhaji Yusuf ya ce masu garkuwa da mutane da suka addabi sassan jihar sun yi awon gaba da ’ya’yansa biyu Alhaji Yunusa Yusuf mai shekara 50 da kanensa Bahago Yusuf mai shekara 48 a ranar 13 ga watan Janairu da daddare, kuma sun ki sako su duk da ya biya su kudin fansa.
Ardo Alhaji Yusuf ya ce ’yan ta’addan sun yi masa waya inda aka yi ta buga ciniki da su kafin aka shirya da su za su a biya Naira dubu 900 kafin a sako su.
Ardo Alhaji Yusuf ya shaida wa Aminiya cewa ba su yi wata-wata ba sai suka kama shanu suka kai kasuwa suka saryar da su don a hada wannan kudi a ceto ’ya’yan nasa. “Amma abin takaici bayan an ba da kudin sai aka samu akasi inda tun ana sa rai har abu ya dawo danye aka kwashe kwana 43 ba su ba labarinsu bayan an biya kudin fansa amma har yanzu ba a ji duriyarsau ba,” inji shi.
Ardon ya ce ’ya’yansa magidanta ne suna da mata da ’ya’ya da yawa wadanda su ma duk sun shiga halin kunci da damuwa, inda jikokinsa suke ta yi masa kuka suna neman ganin iyayensu.
Binciken Aminiya ya gano cewa wadansu da ake zargin bakin Fulani ne dauke da bindigogi kirar AK47 suke yi wa garuruwan da ke kananan hukumomin Chikun da Kachiya wannan mugun aiki, inda suka fara ne da satar shanun Hausawa da na Gbagi, suna cewa suna yin katsalandar ga hanyar cin abincin Fulani ta gado. Daga bisani sai suka fara yin fashi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, kafin likkafa ta yi gaba su fara satar shanun Fulanin, sannan kusan shekara guda da ta wuce suka kai ga garkuwa da ’ya’yan Hausawa da Gwari sannan a baya -bayan da ’yan uwansu Fulani.
Wata majiya mai karfi ta shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar suna da yawa kusan mutum 500 majiya karfi karfi da tsofaffi, maza da mata da yara inda suke zaune a tsakanin garuruwan Gwagwada da Rijana da Chikun da Buruku da Damba da Kasaya da Sabuwar Kasuwa da Kwashere da sauransu.
Ana zargin suna cikin wadanda aka koro daga dajin Kamuku da ke karamar Hukumar Birnin Gwari ne, dajin da ya hada da jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Zamfara.
Bincike ya gano cewa dalilin komawarsu yin garkuwan da mutane shi ne idan sun saci shanu suna samun matsalar safara da sayar da su a kasuwa. Sai suka sauya salo inda suka fara yin garkuwa da ’ya’yan masu dukiya da masu shanu ta yadda wanda aka yi garkuwa da nasa zai kwashi shanun da kansa ya kai kasuwa ya sayar ya kai musu kudin.
Majiyar ta ce Dagacin Gwagwada wanda dan kabilar Gbagi ne Mista Adamu Daniel ya gudu a watanni da suka wuce saboda fargaba.
A kwanakin baya jirgin helikwafta na sojan saman Najeriya ya kai farmaki ga barayin mutanen inda aka ce sun koma cikin kogon dutse sun boye.
barayin mutanen sun yi garkuwa da ’ya’yan Alhaji Barde su uku sai da ya biya Naira miliyan biyu da rabi kafin su sako su. Sai wani Alhaji Baffa ya biya Naira miliyan daya kafin a sako dansa. Kuma sun sace dan wani Fasto inda har sai da ya sayar da gonarsa kafin ya fanso shi.
Majiyar ta kara da cewa, ’yan sandan garin Gwagwada ba su wuce 12 ba, ba za su iya katabus ba.’Yan ta’addan suna yawo ne da bindigogi a rataye suna cin kasuwa ko su sha shayi in sun ga dama su biya, wani lokaci kuma su ki biya.
A makon jiya ’yan ta’addan sun yi kwana 10 a jere suna kai farmaki ga kauyen Fulani na Kwashere da ke da kimanin gidaje 50 da mutanensa ke barin garin.
Majiyar ta ce an sanar da tsohon Shugaban karamar Hukumar Chikun Ali Waziri matsalar ta Gwagwada amma shiru har ya sauka daga mulki. Sannan Kantomar riko ta karamar hukumar Hajiya Hadiza an sanar da ita.
Wani mazaunin Rijana da aka sakaye sunansa, ya ce shekara guda ke nan da fara satar mutane a yankin na Rijana. Ya ce an yi garkuwa da mutane a Rijana da dama, kuma an ba da kudi kafin a sako Tafida da Bami Gwari dan Dagacin Gwari an ba da kudi kafin aka sako shi. A gari kuma an kama wasu mata har sai da mutane suka yi karo-karo kafin a sako su. Bayan nan a kauyen Sabon Maro an kama wata matar talaka sai da akayi karo karo aka sako ta.
Ya ce gwamnati ta dauki mataki mako uku da suka wuce an kama mutane har a cikin garin an tafi da su Kaduna. Amma barayin mutanen sun kuma sace wani mai gonar zamani mai suna Mustapa Albarkawa a gonarsa da ke Abakwa lokacin da ya zo kewayen gonarsa mai suna Albarkawa, sai da aka ba da kudi sannan aka sako shi.
Alhaji Husaini Ladugga Kachia daya daga cikin jami’an kungiyar Miyetti Allah ta kasa ya ce mafita ita ce Sarakunan Arewa su a sama wa Filani burtali da labin shanu, sannan masu halin banza su tuba domin a zauna lafiya. Ya yaba wa Agwan Atyap da ke karamar Hukumar Zangon Kataf Dokta Harrison Bungon kan yadda ya tabbatar da zaman lafiya a tsakanin Katafawa da Fulani. “Amma a yankin Bajju da wasu bangarorin karamar hukumar ba a zaman jin dadi. Ya bukaci jami’an tsaro su daina cin zarafin Fulani domin in sun ci karo da Fulanin gaskiya suna matsa musu.
Ya ce ya dace a binciki jami’an tsaro domin a watan Oktoba zuwa Disamba an gano shanu 700 a Kachiya amma ba su san yadda aka yi suka bata ba. Domin karamar hukuma da DPO ba su nemi Miyetti Allah sun yi musu bayani yadda aka yi da su ba, kuma shi ma basaraken yankin Kadara Mista Galadima bai san yadda aka yi ba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna DSP Zubairu Abubakar ya tabbatar da cewa sun farmaki kauyukan da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sannan sun kara motocin sintiri don tabbatar da tsaro.

ADVERTISEMENT