✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kirkiri Masallacin tafi da gidanka a Japan

Wannan ba ainihin motar a kori kura ba ce, a’a masallaci ne kan tayoyin mota,  wanda ke kewaye kan titunan birnin Tokyo, na kasar Japan.…

Wannan ba ainihin motar a kori kura ba ce, a’a masallaci ne kan tayoyin mota,  wanda ke kewaye kan titunan birnin Tokyo, na kasar Japan.

Ana kiran shi da suna masallacin tafi da gidanka, an yi shi ne dauke da wajen da ake sallah mai fadin murabba’in mita 48, wanda yake a bayan motar da za a iya bude shi bayan ta tsaya.

Makasudin gina masallacin shi ne a samar da dama ta tafi da gidanka ga Musulmi su sami tsabtataccen wurin ibada a lokacin da za su halarci gasar wasannin Olympics a birnin Tokyo da za a fara nan da wani lokaci.

Cikin motar da ke yin sallah

 

Masu shirya gasar Tokyon ta 2020 sun fada a ranar Laraba cewa, suna duba duk hanyoyin da za su samar wa kowane addini damar yin ibadarsa yadda ya kamata a lokacin gasar.

A cewar jami’an, akwai masallatai 105 a duk fadin kasar Japan; koda yake, da dama cikinsu kanana ne kuma suna wajen birnin Tokyo ne wanda hakan zai sanya Musulmi cikin matsi wajen yin salloli biyar a rana.

A lokacin da za a fara wasannin a watan Yuli, za a samu isassun wuraren sallah a kauyen musamman domin wasannin da ake kan gina shi a halin yanzu. Koda yake, wasu wuraren wasannin ba za su samu irin wadannan masallatan ba.

(Reuters)