✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kone motar jami’an tsaro a boren Garejin Akinyele

Boren da kanikawa masu gyaran motoci suka yi a karshen makon jiya kan hana su aiki a gefen babbar hanyar Garejin Akinyele a kusa da…

Boren da kanikawa masu gyaran motoci suka yi a karshen makon jiya kan hana su aiki a gefen babbar hanyar Garejin Akinyele a kusa da Ibadan, ya haifar da kone-konen taya a kan hanya tare da kone motar Hukumar Tara Haraji ta Jihar Oyo.

Binciken Aminiya ya gano cewa, sabani kan karbar harajin matsuguni da gwamnati ke yi daga kanikawa da masu facin taya da kokarin tashinsu daga gefen hanya ne ya haifar da boren inda kanikawan suka kori jami’an.

Dirar mikiyar da sojoji suka yi tare da harba bindiga a sama a ranar ce ta kwantar da kazancewar lamarin inda mafi yawan masu boren, (wadanda Yarbawa ne) ’yan gari suka toshe babbar hanyar tsawon yinin ranar suna kone-konen tayoyi da ya haifar da dogon layin abubuwan hawa da ke zirga-zirga daga Kudu zuwa Arewa kafin sojojin su tarwatsa su su bude hanyar.

Ba a samu hasarar rai ba, sai dai wadansu mutane sun samu raunuka a kokarin tsere wa jami’an tsaro. Rufe shaguna da kantuna da ’yan kasuwa suka yi lokacin boren ne ya sa jita-jitar rufe garejin ta bazu cikin gari, lamarin da Shugaban Garejin, Alhaji Yaro Abubakar ya musanta, inda ya ce, “Mahukunta ba su bayar da umarnin rufe garejin saboda wannan bore ba, sai dai jama’a ne suka rufe wuraren da kansu.”

Da yake yi wa shugabannin sassann garejin bayani, jim kadan da wata ganawa da jami’an tsaro a ranar Litinin da ta gabata, Shugaban Garejin na Akinyele Sarkin Gabas Alhaji Yaro Abubakar, ya ce, “Mun gode wa Allah da Ya sa babu hannun mutanenmu( ’yan Arewa) a cikin wannan lamari a daidai irin wannan lokaci da ake samun matsalar tsaro a sassan kasar nan. Saboda haka ina kira da babbar murya ga dukkan direbobi da leburori da kanikawa da ’yan kasuwa da masu abinci da dukkan masu ruwa-da-tsaki ’yan Arewa a wannan gareji su girmama doka da oda kuma su tsame kansu daga shiga cikin kowace irin zanga-zangar da za ta iya tayar da hankali,” inji shi.

Ya ce, “Duk rashin jituwar da ta taso a tsakaninku da jama’ar gari to akwai shugabannin sassa a garejin da ya kamata ku mika kukanku gare su, maimakon daukar doka a hannunku.”

A zantawa da Aminiya Alhaji Yaro Abubakar, ya ce  “Lokacin da aka fara boren na hanzarta sanar da jami’an tsaro halin da ake ciki inda ba su yi wata-wata ba suka iso wannan wuri suka tarwatsa masu boren, muka kawar da tarkacen da suka gitta a kan hanya.” Binciken ya nuna cewa, yanzu haka jami’an tsaro suna can girke a sassan garejin da aka riga aka kori dukkan masu hada-hada a gefen hanya kuma ’yan sandan Jihar Oyo sun tabbatar da kama wadansu mutane da ake zargi da haddasa boren.