✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kone ofisoshin ’yan sanda 5 a Oyo —Kwamishina

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Oyo Mista Chucks Enwonwu ya ce, an kashe jami’an ’yan sanda shida tare da kone ofisoshi biyar yayin zanga-zangar #EndSARS  da…

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Oyo Mista Chucks Enwonwu ya ce, an kashe jami’an ’yan sanda shida tare da kone ofisoshi biyar yayin zanga-zangar #EndSARS  da aka gudanar a jihar.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a Ibadan babban birnin jihar ranar Laraba, ya kuma ce a yanzu haka an tsare mutum tara da ake zargi da aikata laifin kone-kone da sace kayan jama’a a yankunan Iseyin a cikin Karamar Hukumar Iseyin da ke jihar.

An dai gabatar da wadanda ake zargin a gaban ’yan jarida lokacin da Kwamishinan ke yin bayani.

A lokacin da Mista Chucks Enwonwu yake bayyana alhininsa game da kisan Jami’an ’yan sandan ya ce a lokacin da maharan za su kashe  jami’an sun babbake su ne kamar awakai ba tare da sun yi laifin komai ba ga maharan.

Ya ce, mutum shida cikin wadanda aka kama a garin Ogbomoso lokacin zanga-zangar EndSARS a garin, an mika su ga kotu don yanke masu hukuncin da ya dace.

Kwamishinan ya ce, jami’an ’yan sandan na ci gaba da nemo wadanda suka yi wa jama’a kisan gilla tare da sace dukiyoyin jama’a a jihar, kuma nan bada jimawa ba za a nemo su.

A  cewar Kwamishinan ’yan sandan jihar “Jami’an ’yan sanda shida da aka yi wa kisan gilla tare da kone Hedkwatar ’yan sandan ta gundumomi da kone motoci Rundunar ’yan sanda, tare da sace wasu kayan aikin ’yan sanda da makamai duk da niyyar cewa zanga-zanga ake yi amma aka buge da aikata miyagun laifuka.”

A yayin binciken Rundunar ’yan sandan da aka tura yankin lokacin da suka kamo mutum tara da ake zargi da aikata miyagun laifukan lokacin zanga-zangar, an gano alamomin da suka tabbatar da cewa, su suka aikata laifin.

An kama wadanda ake zargin ne ta hanyar samo bayanan sirri kuma ana ci gaba da yin binciken nemo sauran ababen zargin.

Sunayen ababen zargin da Kwamishinan ’yan sandan ya sanar sun hada da: Taoreed Hamsat da aka fi sani da  Shorled mai shekara 26; da Tajudeen Ibrahim da aka fi sani da Aji, mai shekara 40; da Moshood Fatai da aka fi sani da Elewure mai shekara 39 da Musibau Abubakar da aka fi sani da Stainless mai shekara 21.

Sauran sun hada da: Sikiru Aliu mai shekara 25; Fasasi Fatai da aka fi sani da  Lemon mai shekara 24; Isiaka Olaniyi mai shekara 32; Raheem Toheeb da Adeleke Akeem mai shekara 42.

Sai dai Taoreed Hamzat ya amsa laifin da ake zarginsa, inda ya ce ya saci jannareta amma sauran ba su amince da laifin da ake zarginsu ba.