✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kone ’yan fashi biyar kumus

An kone gungun wasu  matasa biyar kumus, a layin Mayne Abenue, wadanda ake kyautata zaton sun gwanance  wajen haurawa gidajen mutane suna yi masu fashi…

An kone gungun wasu  matasa biyar kumus, a layin Mayne Abenue, wadanda ake kyautata zaton sun gwanance  wajen haurawa gidajen mutane suna yi masu fashi a Kalaba,  babban birnin Jihar Kuros Riba.
Mazauna unguwanni masu nisa da ke kwaryar garin Kalaba sun yi fama da hari tare da kwace wayar hannu ko kuma abin wuyan mata.  Wani zubi, masu fashin har ma sukan yi wa mutum yankan rago, idan suka haura gidansa suka iske ba shi da kudi.
Haka nan rana ta baci ga wani dan fashi da ya fizge jakar wata yarinya, bayan ta dawo daga makaranta yana zaton kudi ne, ya fada wani gida da aka biyo shi aka kama shi, nan take aka rataya masa tayar mota da fetur aka kona shi. Ganau kan lamarin, mai suna Abraham Effiong ya shaida wa Aminiya cewa a gabansa aka kona barawon a kofar makarantar Holy Child da ke kan mahadar layin Goldie da Atu da na Mayne Abenue. “Hayaniya ce ta ja hankalinmu, muka fito, amma kafin ka ce ga bakin zare, har matasan sun watsa masa fetur sun kunna masa wuta, wuta na cinsa yana ihu da haka har ya mutu. Ko da ’yan sanda suka iso, ya gama konewa ya mutu, suka dauki gawar suka tafi da ita”. Inji shi.
DSP John Umoh, mai magana da yawun ’yan sandan jihar, ya tabbatar wa wakilinmu labarin.