✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori lakcarori 4 kan lalata da dalibai da wasu laifuka

An kori wasu manyan lakcarori hudu kan yin lalata da dalibai sauran laifuka a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Kogi

An kori wasu manyan lakcarori hudu saboda laifin lalata da dalibai da sauran laifuka a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Kogi (Kogi Poly).

Hukumar gudanarwar Kogi Poly ta kori lakcarorin daga aiki ne bayan samun su da laifuka da suka hada da, “Neman yin lalata da kuma mugunta ga dalibai mata.”

Sauran sun hada da; “Rashin zuwa aiki, rashin ladabi, amfani da takardun bogi, saba doka da kuma karkatar da kudade,” kamar yadda kakakin kwalejin,Uredo Omale, ya sanar ranar Juma’a a Lakwaja.

Sanarwar ta bayyana cewa, daga cikin lakcarorin akwai mutum biyu da suka yi amfani da takardun bogi wajen karbar tallafin Naira miliyan 22.6 da kuma miliyan 21.2 domin samun horo a kasar waje amma suka ki zuwa, suka cinye kudaden.

Akwai kuma wadda aka kora saboda fashin aiki na wata shida, wadda aka umarce ta da dawo da albashin da ta karba na tsawon lokacin da ba ta zuwa aiki.

Hukumar kuma yi wa wasu lakcarori takwas karin girma daga matakin Principal Lecturer zuwa Chief Lecturers.