✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori ma’aikatan Mashal 4000 daga aiki a Gombe

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya kori ma’aikatan Mashal sama da dubu 4000 daga aiki. Wadannan ma’aikata Gwamanatin PDP ta Ibrahim Hassan Dankwambo…

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya kori ma’aikatan Mashal sama da dubu 4000 daga aiki.

Wadannan ma’aikata Gwamanatin PDP ta Ibrahim Hassan Dankwambo ce ta kirkiro su, kuma mafi yawansu ’yan bangar siyasa ne da aka yi musu gyaran tarbiyya sojoji suka ba su horo  kuma suke taimakawa a jihar wajen shawo kan barna.

Tun lokacin da Alhaji Inuwa Yahaya ya zama Gwamna ake ta rade-radin zai kore su, inda wadansu al’ummar jihar ke cewa hakan bai dace ba.

Da ’yan jarida suka tambayi Gwamnan a wancan lokaci kan ko zai tafi da su ko zai kore su, sai ya ce  zai tafi da su kwaskwarima kawai za a yi musu su zama ma’aikata cikakku.

Gwamna Yahaya ya tabbatar musu da cewa su ’yan Gombe ne idan ya kore su yaya zai yi da su, sannan ya kara da cewa zai tafi da su amma zai gyara tsarin inda za a rika samar musu da aikin dan sanda ko soja da sauransu,  amma kwatsam sai aka sanar da korarsu daga aiki.

A wata hira da ya yi da wadansu ’yan jarida a Gombe Gwamna Inuwa Yahaya ya ce ya kore su gaba daya ne saboda siyasa ce ta sa tsohuwar gwamnati ta kafa su don a ci musu mutunci loakcin yakin neman zabe da kuma lokacin zaben da ya gabata.

“Na kore su kuma gwamnati za ta kafa Ma’aikatar Inganta Tsaron Cikin Gida da kuma Kyautata Al’adu da Dabi’u,’’ inji Gwamnan.

Ya kara da cewa kafin korarsu, ya yi zama da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar da Kwamandar Soji da Kwamandar Hukumar NSDSC inda ya shaida musu cewa tsaron rayukan al’umma a hannunsu yake ba a hannun wadansu Mashal ba.

Wani shugaban al’umma kuma mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum, Murtala Usman jajanta wa al’ummar Jihar Gombe ya yi na yadda a kwana 100 na mulkin APC aka fara da korar ’ya’yansu daga aiki.