Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
An kori shugabannin kananan hukumomi saboda rashin sa takunkumi

An kori shugabannin kananan hukumomi saboda rashin sa takunkumi

An kori wasu Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Yobe saboda rashin sanya takunkumin kariyar cutar COVID-19 a wurin taro.

Shugabannin rikon kananan kukumomin sun gamu da gamonsu ne a wurin mataimakin gwamnan jihar wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da cutar a jihar, a wurin kaddamar da kwamitin kula da tsaftar muhallin yankunansu.

Ya kori duk marasa takunkumi daga dakin taron da aka yi a gidan gwamnatin jihar, domin “Ba za ku bata kokarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi ba na kare mutane daga COVID-19”.

Ya nuna takaicin cewa maimakon su zama abin koyi, shugabannin wadanda yawancinsu Darektocin Kula da Ma’aikata ne a kananan hukumomi sun bige da saba dokokin kariyar cutar.

Don haka ya ce, “Zan dakatar da taron nan idan har a matsayinku na jagorori ba za ku bi umarni mai sauki ba kan kiyaye COVID-19”.