✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori sojoji 3 kan kasancewa ’yan kungiyar asiri

Rundunar samar da zaman lafiya ta Opration Lafiya Dole da ke yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabas ta sanar da korar sojojinta uku…

Rundunar samar da zaman lafiya ta Opration Lafiya Dole da ke yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabas ta sanar da korar sojojinta uku da ake zargi da kasancewa a cikin kungiyar asiri da ’yan sanda suka kama  a makon jiya.

Babban Kwamandan Rundunar Manjo Janar Adeniyi ne ya shaida wa manema labarai haka, inda ya ce “Wadannan sojoji uku tuni muka mika musu takardar sallama daga aikin soja, domin ba a san soja da aikin cin amanar kasa ba, kuma bayan sallamarsu mun mika su ga ’yan sanda don daukar mataki na gaba.’’                                                                                                                                                     Idan za a iya tunawa a karshen makon jiya ne Rundunar’Yan sandan Jihar Borno ta kama ’yan kungiyar asiri 25 a wani samamen da ta kai wani gidan  shakatawa a wajen garin Maiduguri.

Da yake gabatar da su ga manema labarai, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Borno Muhammad Ndatsu Aliyu, ya ce, “Rundunar ta samu nasarar kama wadanda ake zargin ’yan kungiyar asirin su 25 ne a wani gidan shakatawa da ke Unguwar Abujan Talakawa, da misalin karfe 2:00 na dare, tare da hadin gwiwar Kungiyar Maharba da sauran jami’an tsaro, an kuma kama su ne tare da wasu makamai da kayayyakin asirinsu kamar bakaken tufafi da jarkunan jinin mutane, da  da katin shaidar da ke nuna cewa wannan kungiyar asiri ce.”

Kwamshinan ya kara da cewar, “A cikin mutum 25 din da muka kama akwai sojoji 3 da daliban Jami’ar Maduguri 8 da kuma na Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Ramat da ke Maiduguri su 4, kuma an kama su ne suna gudanar da wasu raye-rayensu na tsafe-tsafe.”  Kwamishinan ya ce suna nan sun ci gaba da bincike a kan kuma da zarar sun kammala za su mikasu kotu don fuskantar shara’a.

Sharri aka min- Daya daga cikin wadanda ake zargi

Daya daga cikin wadanda ’yan sandan suka kama mai suna Muhammed Ibrahim, ya shaida wa wakilinmu cewar, “Ban san hawa ba ban san sauka ba, na san dai ni ina karatu ne a Jami’ar Maiduguri kuma mun kammala jarrabawa ce shi ne sai muka hada biki don murnar kammala makaranta, shi ne muka zo nan otel din Bagani, muna cikin shakatawarmu sai muka ga jami’ai sun zo sun kama mu ba laifin tsaye balle na zaune,  suka kawo mu nan. Kuma wannan da aka ce jini, ba jini ba ne ruwan zobo ne muka hada da wasu abubuwa muke sha, sannan ba ma amfani da bakaken kaya kamar yadda aka fada.’’