✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori ‘yan sandan da suka kashe barayin wayar salula

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kori ‘yan sandan nan hudu da suka kashe wasu mutum biyu da ake zargi da fashi sannan aka garkame…

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kori ‘yan sandan nan hudu da suka kashe wasu mutum biyu da ake zargi da fashi sannan aka garkame su a gidan kaso.

Wani fefan bidiyo da ya karade kafar sada zumuntar zamani ya nuna yadda ‘yan sandan suka harbe wadanda ake zargin ‘yan fashi ne bayan sun kame su sun sanya su a mota.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaidawa Aminiya cewa bayan umarnin da Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Zubairu Mu’azu, ya bayar na kame ‘yan sandan hudu an kuma ladabtar da su bayan gudanar da bincike inda aka kore su daga bakin aiki ya ce, an gurfanar da su a kotun Ikoyi a Legas “An dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan gobe”.

Tsofaffin ‘yan sandan su hudu sun hadar da Insfekta Fabiyi Omomayara da Sajan Olaniyi Solomon sai Sajan Solomon Sunday da Kufural Aliyu Mukaila.