Da Dumi Dumi

An kubutar da daliban da aka yi garkuwa a Kaduna

Rundunar sojojin Najeriya ta kubutar da daliban makarantar Sakandaren Gwagwada da ke Karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, wadanda aka yi garkuwa da su a ranar 3 ga watan Oktoba 2019.

Rundunar ta kuma samu nasarar kashe masu garkuwa da mutane hudu tare da raunata wasu da dama sannan suka kwato makamai a hannun su, ana zargin suke yin garkuwa da ,mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin ta daya KanalEzindu Idima, ne ya sanar da hakan yau Juma’a.

Share