✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kubutar da limaman coci 5 da aka yi garkuwa da su a Ogun

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta sami nasarar kubutar da daukacin limaman cocin Ridim su biyar da aka yi garkuwa da su a ranar Alhamis…

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta sami nasarar kubutar da daukacin limaman cocin Ridim su biyar da aka yi garkuwa da su a ranar Alhamis da ta gabata.

An dai fara kubutar da daya daga cikin limaman cocin ridim guda biyar da aka yi garkuwa da su a kan babbar hanyar nan ta Binin daga Shagamu wanda ta kubuta. Uwargida Ibelegbo Chidinma wacce ita ce kadai mace a cikin manyan limaman cocin biyar da aka yi garkuwa da su ta samu kubuta ne ba tare da ko kwarzane a jikinta ba, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi ya sanarwa Aminiya labarin kubutar da matar, ya ce izuwa yanzu rundunar na shirin kai matar cocin ta ridim da ke kan babbar hanyar nan ta Legas daga Ibadan a jihar Ogun.

Kafin kubutar da sauran limaman cocin hudu, DSP Abimbola ya ce yanzu haka muna tare da matar a babban ofishin mu da ke Eleweron muna shirin kai ta cocin ridim, kana jami’an mu na gab da ceto ragowar limaman cocin hudu da ke hannun masu garkuwar wadanda bayanai suka tabbatar mana ‘yan garkuwar sun rarraba su a tsakanin su kana suna sassauya maboyar su a dajin da suke tsare da su”.

Shugaban cocin ta ridim Fasto Adeboye ne ya sanar da rahoton garkuwa da manyan limaman cocin nasu a  jiya Juma’a inda ya ce an yi garkuwa da su ne a lokacin da suke kan hanyar su ta halartar taron limaman cocin daga Kudu maso Gabashin kasar nan inda aka yi garkuwa da su akan hanyar Binin daga Shagamu a jihar Ogun.