Da Dumi Dumi

An mika wa PSG kambun gasar Ligue 1

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG

Hukumar kula da gasar kwallon kafa ta Faransa ta mika wa kungiyar kwallon kafa ta PSG kambun gasar Lique 1 ranar alhamis bayan da ta yanke hukuncin katse gasar dalilin cutar coronavirus.

Kungiyar ta PSG ce ke sama a teburin gasar da maki 21 gaba da kungiyar Marseille lokacin da aka sanar da dakatar da wasanni bayan bullar cutar coronavirus a kasar.

Zuwa yanzu dai cutar ta kashe sama da mutane 24,000 bayan bullarta a tsakiyar watan Maris a kasar ta Faransa.

Sanarwar ta zo ne bayan da Firaministan kasar, Eduoard Philippe, ya sanar a ranar Talata cewa ba zai yiwu a koma wasanni ba a dalilin cutar.

Hukuncin hukumar kwallon ta Faransa ya saba da na takwararta ta kasar Holland ta yanke inda ta sanar da cewa babu wanda ya lashe gasar a bana.

ADVERTISEMENT

Wasanni goma ne dai suka rage a kammala gasar ta Ligue 1 inda zakarun na bana suke da kwantan wasa da kungiyar Strasbourg.

Kungiyar ta lashe gasar ne da kusan maki biyu da rabi a kan ko wanne wasa da ta buga a bana

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya