✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An mika wa PSG kambun gasar Ligue 1

Hukumar kula da gasar kwallon kafa ta Faransa ta mika wa kungiyar kwallon kafa ta PSG kambun gasar Lique 1 ranar alhamis bayan da ta…

Hukumar kula da gasar kwallon kafa ta Faransa ta mika wa kungiyar kwallon kafa ta PSG kambun gasar Lique 1 ranar alhamis bayan da ta yanke hukuncin katse gasar dalilin cutar coronavirus.

Kungiyar ta PSG ce ke sama a teburin gasar da maki 21 gaba da kungiyar Marseille lokacin da aka sanar da dakatar da wasanni bayan bullar cutar coronavirus a kasar.

Zuwa yanzu dai cutar ta kashe sama da mutane 24,000 bayan bullarta a tsakiyar watan Maris a kasar ta Faransa.

Sanarwar ta zo ne bayan da Firaministan kasar, Eduoard Philippe, ya sanar a ranar Talata cewa ba zai yiwu a koma wasanni ba a dalilin cutar.

Hukuncin hukumar kwallon ta Faransa ya saba da na takwararta ta kasar Holland ta yanke inda ta sanar da cewa babu wanda ya lashe gasar a bana.

Wasanni goma ne dai suka rage a kammala gasar ta Ligue 1 inda zakarun na bana suke da kwantan wasa da kungiyar Strasbourg.

Kungiyar ta lashe gasar ne da kusan maki biyu da rabi a kan ko wanne wasa da ta buga a bana